Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje tare da hadin guiwa da wasu kamfanoni masu zaman kansu wajen sun himmatu wajen mayar da wuraren da akanyi watsi dasu, inda ake gina rumfunan kasuwanci a wuraren da suka Dace, kamar yadda aka sani da yawa wasu wuraren anyi watsi dasu wasu ma sun zama kufai. Musamman gine ginen Gwamnati da aka daina amfani dasu irin Kamfanin buga Jaridu naTruimph, wanda aka mayar da shi wurin kasuwanci canjin kudaden kashen waje.
Jawabin haka ya fito daga bakin guda cikin Dattijan kasuwar kantin kwari, mai yawan fashin baki kan cigaban ‘yan Kasuwa da kasuwanci a Jihar Kano Alhaji Muhammad Abdullahi Mai Dubji alokacin da yake karin haske kan cigaban da aka samu, musamman samar da daruruwan rumfuna wanda kananan da manyan ‘yan Kasuwa suka samu wuraren gudanar da harkokin cinikinsu na yau da kullum.
Mai Dubji ya tabo batun Tsohon Otal din Daula wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano Alhaji Audu Bako ya Gina, Kuma zuwa yanzu an shafe sama da shekara 20 da daina amfani dashi, shima yanzu an rusheshi inda ake shirin mayar da shi wata katafariyar cibiyar kasuwanci wadda aka tsara samar da Bankuna, Otal irin na zamani, Masallachin Juma’a da sauran abubuwan da zasu kara taimakawa wajen samar wadata da yalwar arzikin Kano.
Alhaji Muhammad Mai Dubji yace Samar da wadatattun kantuna a Kasuwar Kanti kwari ne ya kawo karshen batun kudin takalmi da dillalan rumfuna ke kakabawa ‘yan Kasuwa a lokacin da ‘yan Kasuwar ke bukatar samun rumfunan gudanar da harkokin kasuwanci.
Shi ma batun gidan adana namun daji (Zoo) wanda yanzu ya zama tsakiyar gari kuma hakan na zaman barazana ga al’ummar dake zagaye da gidan, hakan tasa Gwamnatin yin duban tsanaki duba yadda za’a sauyawa gidan adana namun dajin wuri wanda zai dace ingantacin rayauwar dabbobin, wanda ake fatan mayar da tsohon wurin zuwa cibiyar ciniki ta zamani.
A karshe Dattijan arzikin ya jinjinawa kokari na Gwamna Ganduje tare da taimakon masu kishin cigaban Jihar Kano, musamman Dattijan kasuwar kantin kwari da kewaye, sannan ya kara tabbatar da kyakkyawar fahimta da aka samu a Kasuwar wanda hakan ya kara samar da yanayiai kyau tsakanin ‘yan Kasuwar da bakinsu.