Daga Rabiu Ali Indabawa
Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta bai wa Sanata mai wakiltan Borno ta kudu, Ali Ndume, wanda aka tsare a kurkuku tun ranar Litinin beli. Alkali Okon Abang a hukuncin da ya yanke ranar Juma’a ya ce ya yanke shawarar bai wa Sanata Ndume beli ne saboda tarihinsa na mai halayya mai kyau, amma ba don uzurorin da ya gabatar ba.
Alkali ya bashi beli ne kafi kotun daukaka kara ta saurari karar da Ndume ya shiga ranar Litinin domin kalubalantar hukuncin jefa shi kotu kan gaza kawo Maina kotu. Ya umurci Sanatan ya kawo wanda zai tsaya masa kuma ya kasance mazauni Abuja kuma mai dukiya a Abuja.
A cewar Alkali, wanda zai tsayawa Sanatan wajibi ne ya rantse cewa zai sadaukar da dukiyarsa idan Sanatan ya gudu. Bayan haka, Alkalin ya umurci Sanatan ya sallama fasfot dinsa ga magatakardar kotun.
Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran lamuran fansho, ya gurfana a kotu kan zargin almundahanar makudan biliyoyi. A ranar 18 ga Nuwamba, 2020, Alkali Abang ya janye belin da ya bai wa Maina kuma ya ba da umurnin daure shi. Bayan an nemi Maina an rasa, Alkali ya ce a garkame Ndume a kotu maimakonsa ko ya biya kudi Naira miliyan 500.