Dan Majalisar da ke wakiltar Mazabar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume, ya fada komar Babbar Kotu a Abuja bayan da tsohon Shugaban Hukumar Kula da ’Yan Fansho na qasa, Abdurrasheed Maina, ya kasa bayyana a gaban kotun, duk da cewa, Sanata Ndume din ne ya tsaya ma sa wajen amsar belinsa, lamarin da ya sanya kotun ba ta da wani zabi wanda ya wuce ta aike da sanatan gidan yari.
Tun a ranar Juma’a Ndume ya fada wa Babbar Kotun ta Tarayya da ke Abuja cewa, ba shi da masaniyar wurin da tsohon shugaban kwamitin musamman mai suna ‘Reform Task Team’ kan aikin fansho, ya ke.
Jigon a jam’iyyar APC din ya na a matsayin mai belin Maina, wanda Hukumar Yaqi da Yi Wa Tattalin Arzikin Qasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da kan tuhume-tuhume 12 da su ka hada da halasta kudaden haram, wanda ya hada da Naira biliyan biyu.
Bayanai da a ka tattara sun bayyana cewa, Maina bai halarci kotun sau uku a jere a cikin mako guda ba. Dangane da qa’idoji da sharuddan belin da Alqali Okon Abang ya bayar a watan Janairun 2020, Ndume ya sha rantsuwar kotu cewa, zai riqa kawo wanda a ke qarar zuwa kotu duk ranar da za a fara shari’ar, sannan ya ba wa kotun takardun mallakar gidansa da kudinsu ya kai Naira miliyan 500 a yankin da a ka zaba na Abuja a matsayin garanto.
Da alqalin ya tambaye shi ko ya san inda wanda a ke tuhumar ya ke, Ndume ya ce, “Ya Mai Shari’a, dole ne na yi iqirarin cewa, ban sani ba.”
Dan majalisar, wanda ya tuna cewa, ya amince ya zama wanda zai zama matsaya wa Maina ne bayan roqon matar da wanda a ke qara da kawunta su ka yi ma sa, inda ya kuma ce, “ban hangi wannan yanayin ba, Ya Mai Shari’a.”
Ya jaddada cewa, bai san gidan Maina a Abuja ba, amma ya san wanda ke Kaduna. Sai sanatan ya roqi a ba shi qarin lokaci, domin ya nemo wanda a ke qarar.
Mai shari’a Abang ya ce, kasancewar bai gabatar da Maina ba, wanda a ka yi imanin ya tsallake belinsa kuma ya kasa nuna dalilin da ya sa ba za a hana shi beli ba, ya bayar da umarnin a tsare Ndume kuma kada a sake shi sai kawai idan ya cika kowanne daga cikin sharuda uku.
Na farko shi ne cewa, ya biya kudin belin Naira 500 a cikin Asusun Tarayya na Gwamnatin Tarayya kuma ya gabatar da shaidar wannan biyan a kotu ko Gwamnatin Tarayya ta sayar da kadarorinsa da ke Asokoro a Abuja, wanda Ndume ya yi alqawarin bayarwa a matsayin jingina tare da gabatar da shaidar sayarwa da biya na Naira miliyan 500 da a ka gano a cikin asusun Tarayya ko shi (Ndume) ya gabatar da Maina, wanda a ke jin cewa, yanzu ya arce daga belin kotu.
Rufe bakin alqalin ke da wuya kuwa, sai jami’ai su ka damqe Sanata Ndume a dakin shari’ar, inda su ka yi awon gaba da shi zuwa gidan yari da ke Kuje a yankin babban birnin Tarayyar Nijeriya da ke Abuja, inda zai cigaba da zama har sai ya cika sharadin da mai shari’ar ya gindaya ma sa.
Idan dai za a iya tunawa, tun a shekarar bara kotun ta bayar da belin Maina bisa wasu tsauraran sharudda, ciki har da kawo mai riqe da muqamin kujerar sanatan, amma ya shafe watanni a tsare ba tare da an samu wanda zai tsaya ma sa ba.