Majalisa Na Fama Da Rashin Tallafin Kudade, Inji Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya bayyana cewa,Majalisar ta su, tana ta fama ne wajen yunkurin aiwatar da abubuwan da suka rataya a wuyanta, duk da karancin kudaden da take fuskanta. Duk da kururuwar da wasu suke ta yi na cewa wai, ana kashe ma Majalisar kudade masu yawa.

Saraki ya yi wannan kalaman ne a sa’ilin da ya kaiwa sashen lura da ayyukan Majalisar (NASC), ziyara a ranar Laraba.

Babban mai taimakawa Sanata Sarakin ne a kan harkokin ‘yan Jaridu, Mista Chuks Okocha, ya yi bayanin ziyarar ta Saraki ga wannan sashen filla-filla.

A cewar bayanin, Sanata Bukola Saraki, ya yi wannan kalamin ne a lokacin da yake mayar da amsa kan bukatar da wannan sashen ya yi masa, na a samar masa da tabbataccen mazauni a ginin Majalisar.

“Daya daga cikin abin da nake gani a yau shi ne, matsalar karancin kudade, duk kuwa da kururuwar da ake ta yi a cikin kasarnan, wanda ke nu ni da cewa wai ana kashewa Majalisa kudade masu yawa. Amma mu a ‘yan shekarun nan mun san matsalolin da muke fuskanta. Mun san yanda muka kukkulla wajen tafiyar da aikace-aikacen mu da dama, mun kuma san dalilan da suka hana mu iya aiwatar da wasu ayyukan namu saboda karancin kudade.

“zuwa yanzun, ina mai farin cikin shaida maku cewan, duk da karancin kudin da muke fuskanta, wannan Majalisar tamu wacce ita ce karo na takwas a wannan kasa tamu, ta zarta duk wadanda suka gabace ta a cikin shekaru biyu, wajen zartas da ayyuka duk kuwa da karancin kudin da muke fuskanta. Muna kuma da tabbacin nan gaba mutane za su fahimci irin dimbin ayyukan da muka yi masu, da kuma yanda muka yi ta kulle-kulle da gande-gande wajen ganin mun aiwatar masu da wadannan ayyukan,” in ji Saraki.

“Akwai babban aiki a gabanmu, wajen sanya mutane su yaba wa ayyukan da Majalisa ke yi masu a tsari irin na Dimokuradiyya.

Tun da farko, Shugaban hukumar ta NASC, Dakta Adamu Fika, ya koka ne a kan cewa,har yanzun hukumar ta su a gidan haya ne take gudanar da ayyukan na ta, duk da tsadar wajen da take zama din a cikin na shi.

A nan ne, sai ya yi kira ga Shugaban Majalisar da ya taimaka a gina masu wani matsugunin da ya dace da su a cikin harabar Majalisar.

Exit mobile version