Bello Hamza" />

Majalisa Ta Dage Dawowa Saboda Mutuwar Memba

Majalisar Dattijai ta dage zamanta saboda mutuwar ‘yar majalisar wakilar, Funke Adedoyin.

Funke Adedoyin, wadda ke wakiltar jihar Kwara ta rasu ne ranar Jumma’a da rana a garin Abuja tana da shekara 56 a duniya.

Wani dan majalisa daga jihar Kwara, mai suna, Razak Atunwa, ya bayyana cewa, Misis Adedoyin ta rasu ne sakamakon cutar kansa.

Majalisar dattijai ta dage zaman nata ne bayan zaman awa daya data yi a zaman ta na farko bayan hutun makwannin 10 da ta tafi.

Ita ma, majalisar wakilai da ta dawo zaman nata ranar Talata ta kuma dage zaman na take saboda karrama ‘yar majalisar da ta rasu.

Majalisar kasar ta tafi hutu ne a ranar 24 ga watan Yuli bayan da aka fuskanci takaddamar sauya sheka da kuma shirye shiryen zaben fidda gwani na jam’iyyu, da farko an shirya za su dawo ne a ranar 25 ga watan Satumba daga baya suka dage dawowar zuwa ranar 9 ga watan Oktoba.

Bayan bude zaman na jiya, shugaban Majalisar, Dakta Bukola Saraki ya jagoranci ‘yan majalisar wurin gabatar da addu’a ga marigayyiyar daga nan ne suka shiga taro na musamman na shugabannin jam’iyyar wanda aka sakaya.

Bayan taron sirrin ne, Dakta Saraki ya kuma karanto wasu wasiku da shugaban kasa ya rubuto wa majalisar, bayan nan ne Sanata Ahmed Lawan ya bukaci majalisar ta tsaya ta kuma yi tsit na minti daya don karrama mamaciyar. Ya kuma bukaci majalisar ta dage zamanta na ranar kamar dai yadda al’adar majalisar kasa yake. ‘Yan majalisar sun yi kuri’ar amicewa da wadannan bukatun ta hanyar aminceman wa da murya, a kan kuma dage zaman a dai dai karfe 12:19 na rana.

Exit mobile version