Daga Khalid Idris Doya
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince tare da tabbatar da nadin Mista Haliru Nababa a matsayin Babban Yarin kasa, wato Kwantirola Janar na hukumar gidajen gyara halinka a Nijeriya wato ‘Nigerian Correctional Serbice’ (NCS).
Tabbatar da Nababa kan wannan kujerar na zuwa ne bayan rahoton da kwamitin majalisar dattawa kan kula da harkokin cikin gida a karkashin jagorancin Sanata Kashim Shettima (APC, Borno ta Tsakiya) ya gabatar a zaman majalisar na jiya.
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya aike da wata wasika ga majalisar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2021 inda ke neman majalisar datttawan da su tabbatar da nadin Nababa a matsayin shugaban hukumar kula da gidajen yarin Nijeriya.
Da ya ke gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Sanata Kashim Shettima, ya ce, Nababa bayan masa gwajin tantancewa sun gamsu da amincewa da shi bisa tanede-taneden sashin doka na 3(2) da ke makale a cikin dokar hukumar NCS na 2019.
Sanatan ya ce, babu wata takardar korafi a kansa, kuma shi din ba dan wata jam’iyyar siyasa bane don haka ya kasance mutum mai nagarta da dattako.
Ya ce, a lokacin da suka zaunar da Nababa domin masa tambayoyi a kokarinsu na tantance shi, sun iya fahimtar yana da kwarewa da cikakken sani kan halin da gidajen yarin Nijeriya ke ciki tare da matsalolin da suke akwai, don haka ya cancanci zama a wannan kujerar.
Da yake mara baya wa zabin shugaban hukumar, tsohon Ministan kula da harkokin cikin ida, Sanata Abba Moro (Mai wakiltar mazabar Benue ta Kudu, ya bayyana cewar, “Nababa ya yi aiki a karkashina, a lokacin ma da gidajen yari ke matukar fuskantar kalubale daban-daban, lokacin an kai hari da farmaki ga gidajen yari da dama a sassan Nijeriya. Saboda kwarewarsa da gogewarsa ya iya jan ragamar matsalolin tare da shawo kan kalubalen da suke jibge. A lokacin da ya zo domin tantance shi, ko kadan ban ji dar a kansa ba. Ya kasance wanda zai iya jan ragamar hukumar nan yadda ya dace.”
Duk a jiya, majalisar ta kuma tura bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman tabbatar da nadin Salamatu Suleiman a matsayin shugaban hukumar kare hakkin bil-adama da wasu mambobi 15 zuwa kwamitin da suka dace.
Buhari dai na neman majalisar ta tabbatar da Joseph Onyemaechi, Mohammed Abubakar, Timi Asiwaju, Sunny Daneil, Idayat Omolara Hassan, Beatrice Jeddy Agba, Umar Salisu, Dafe Adesida, Ahmad Finngilla, Kemi Okeowo, Agabaidu Jideani, Nella Rabana, Azubuike Nwakwenta, Jamila Isa da Farfesa Anthony Ojukwu a matsayin mambobin hukumar.
Shugaban majalisar dattawan, Dakta Ahmad Lawan, ya hannanta bukatar zuwa gaban kwamitin shari’a, hakkin bil-adama da batutuwan da suka shafi shari’a, domin masa bita na musamman da nazartar bukatar yadda ya dace.
Kwamitin dake karkashin Sanata Opeyemi Bamidele, an ba su wa’adin mako biyu da su kammala tantancewa tare da gabatar da rahotonsu a gaban majalisar dattawan.