Umar A Hunkuyi" />

Majalisa Ta Tabbatar Da Nadin Dongban-Mensem Shugabar Kotun Daukaka Kara

A jiya Alhamis ce Majalisar Dattijai ta tabbatar da nadin Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, a matsayin shugabar kotun daukaka kara.

Hakan ya zo ne a daidai lokacin da shugaban Majalisar Dattawan, Ahmad Lawan, ya yi alkawarin cewa majalisun kasan za su bayar da hadin kan da ake bukata wajen kawo gyara a sashen na shari’a.

Tabbatar da Mai shari’a Monica Dongban-Mensem, a matsayin shugabar kotun daukaka karan ya biyo bayan gabatarwa da tantancewa da kwamitin shari’a da kula da hakkin dan adam na majalisar ne ya yi.

Sanata Micheal Opeyemi Bamidele (Ekiti ta tsakiya), wanda shi ne shugaban kwamitin.

A cikin wata wasika da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar ya bukaci da majalisar ta amince da nadin da ya yi wa Mai shari’a Dongban-Mensem, a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka karan.

A cikin rahoton kwamitin na Bamidele, ya yi nuni da cewa, Mai shari’a Dongban-Mensem; “Tana da kwarewa, cancanta da sanin makaman aikin, sannan kuma tana da halayen da suka cancanci shugabanci a fannin na shari’a ta yanda za ta iya gudanar da ayyukan shugabantar kotun daukaka karan.”

Cikin jawabinsa na taya ta murna, Lawan ya karfafa bukatar kawo sauyi a sashen na shari’a cikin hanzari.

Yana mai cewa: “Ina yin tarayya da sauran abokanan aiki na da suka bayar da gudummawarsu a wajen hada rahoton wannan kwamitin, gami da fayyace dukkanin halayen kirki da cancanta na wacce aka nada.

“Sashen shari’a yana bukatar sauyi. Majalisar wakilai ta tarayya da majalisar Dattijai musamman a shirye suke kuma a kowane lokaci wajen bayar da goyon bayan majalisun a kan duk wani sauyin da ya kamata wanda ake da nufin kawo wa.

“Tsarin shari’a a kasar nan tilas ne ya kasance yana kare marasa karfi, musamman a tsakankaninmu. Wannan kuma shi ne ma’anar shari’a, ba tare da hassadar masu karfi da masu mulki ba.

 

Exit mobile version