Majalisar Wakilai ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan gilla da aka yi wa wasu mutane 13 da ba su ji ba ba su gani ba a Unguwan Rimi Basawa da ke karamar hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Majalisar ta umurci kwamitinta na wucin gadi da ke aiki kan kalubalen tsaro a jihar Filato da ya gudanar da bincike na musamman kan yadda ake ci gaba da kashe matafiya a hanya daya tare da bayar da rahoto cikin kwanaki 14.
- Barau Ya Nisanta Kansa Daga Kiraye-kirayen Ya Zama Mataimakin Tinubu A Zaben 2027
- Shugabannin PDP Sun Ziyarci INEC Kan Neman Sanin Ka’idojinta
Wannan kudiri ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Sabon Gari ta jihar Kaduna ya gabatar a karkashin al’amuran da ke bukatar kulawar gaggawa na majalisar, Sadiq Abdullahi, a zauren majalisar ranar Talata.
Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar, Abdullahi ya nuna matukar damuwarsa kan kisan da aka yi wa matafiyan a ranar Juma’a, a lokacin da suka bata kan hanyarsu a yayin da suke tafiya don halartar wani daurin aure a karamar hukumar Mangu.
Ya ce, wadanda aka kashen, ba su dauke da wani makami, kawai suna kan hanyarsu ne ta zuwa daurin aure, wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai musu hari tare da kashe su, lamarin da ya jefa ‘yan uwan matafiyan cikin jimami.