Daga Sulaiman Ibrahim,
Majalisar dokokin kasa ta yi wa dokar zabe gyara da wani tanadi da ya baiwa jam’iyyun siyasa damar tsara yadda za a gudanar da zaben fidda gwani.
Hakan ya biyo bayan sake gabatar da kudirin ne a majalisar dattawa da ta wakilai da Sanata Yahaya Abdullahi da na wakilai Abubakar Hassan Fulata suka gabatar a gaban zauren majalisar a ranar Laraba.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da daftarin dokar da aka amince da shi a shekarar da ta gabata kan batun samar da tsarin zabukan fidda gwani na jam’iyyun siyasar.
Gyaran dokar ta bayyana cewa; “Jam’iyyar siyasa da ke neman zabar ‘yan takarar zabe a karkashin wannan kudiri za ta gudanar da zaben fidda gwani na masu neman tsayawa takara a dukkan mukaman zabe, wanda hukumar INEC za ta sanya ido a kai.”
Shugaban kasar ya ce zai amince da kudirin dokar zabe idan ‘yan majalisar suka bayar da zabin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasar.