Majalisar wakilan Nijeriya ta cimma matsayar gudanar da bincike dangane da makudan kudaden da gwamnatin tarayya ta biya kwangilolin magance matsalar rashin tsayayyar wutar hasken lantarki a kasar. Daya daga cikin ‘yan majalisar wakilan Honorabul Sada Soli Jibiya ne ya gabatar da kudurin a wannan Alhamis, da ya samu amincewar daukacin takwarorinsa.
Majalisar ta ce za a binciki tsohuwar gwamnatin ta Olusegun Obasanjo wacce ya jagoranta daga 1999 zuwa 2007, domin bada bahasi kan dala biliyan 16 da gwamnatin ta yi ikirarin kashewa kan inganta wutar lantarkin.
Binciken majalisar wakilan zai kuma fadada bin kwakkwafin zuwa kan gwamnatocin Marigayi Umar Musa ‘Yar Adua, Goodluck Jonathan da kuma gwamnatin mai ci karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.
A shekarar 2008 majalisar wakilan Nijeriya ta taba kaddamar da bincike kan dala biliyan 16 da tsohon shugaban kasar Obasanjo wanda ya yi ikirarin kashewa don inganta lantarki ba tare da ikirarin ya tabbata ba.
A wancan lokacin, tsohuwar gwamnatin ta ce zuba makudan kudaden a fannin lantarkin zai samarwa da Nijeriya karfin wutar da zai kai Megawatts dubu 40 a shekarar 2020.
Har yanzu dai samar da hasken lantarki batu ne da ‘yan siyasar Nijeriya ke amfani da shi wajen neman kuri’a yayin yakin neman zabe, duk da ikirarin gwamnatocin da suka gabata, na zuba makudan kudade a fannin, ba tare da an ga sahihin sakamako ba.