Shugaban kwamitin kula da harkokin Sojoji na majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ya shaida cewar hadakar Kwamitocin Majalisar na Soja, sojan sama da ta ruwa da yiyuwar su fara tantance zababbun sabbin shugabannin hukumomin tsaro a wannan makon da muke ciki.
Sanata Ndume ya bayyana hakan ne lokacin da ke amsa tambayoyi daga jaridar The Nation a Abuja.
Idan za ku iya tunawa dai a ranar Laraba ne shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya tura bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiko na neman Majalisar ta amince da sabbin zababbun shugabannin hukumomin tsaro zuwa gaban kwamitocin majalisar kan soji, sojin sama da ta ruwa domin gudanar da aikin da ya dace a kai.
Lawan ya baiwa kwamitocin mako biyu da su kammala gudanar da ayyukan da aka ba su tare da gabatar da rahoton aikin nasu a gaban majalisar.
LEADERSHIP A YAU ta nakalto cewa sabbin zababbun shugabannin hukumomin tsaron da Buhari ya zaba sun kunshi: Manjo Janar Lucky Eluonye Onyenuchea lrabor a matsayin (shugaban ma’aikatar tsaro); Manjo Janar Ibrahim Attahiru a matsayin (Shugaban sojojin Nijeriya); Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, (Shugaban sojin ruwa); da kuma Air bice Marshal Isiaka O. Amao a matsayin shugaban sojin sama.
Sun canji tsohon Shugaban ma’aikatar tsaro Janarar Abayomi Olonisakin; tsohon Shugaban Sojoji Lt-Gen. Tukur Buratai; tsohon Shugaban sojin ruwa bice Admiral Ibok Ete Ibas da kuma tsohon Shugaban sojin sama Air Marshal Sadikue Abubakar.
Da ya ke amsa tambayoyin Sanata Ndume ya lura kan cewa ba a bayyanar jama’a za su tantance Shugabannin hukumomin tsaron ba.
Ya kuma ce za dai su fara aikin tantancewar a wannan makon tun da an baiwa kwamitocin nasu mako biyu ne kawai da su gabatar da rahoton aikinsu.
Ya yi alkawarin cewa za su ke sanar da jama’a halin da ake ciki dangane da wannan aikin da aka daura musu.