Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Haramta Wa Jiragen Ruwa Zuwa Koriya Ta Arewa

Majalisar dinkin duniya ta haramtawa wasu jiragen ruwa shiga tashoshin jiragen ruwa a duk faɗin duniya saboda jigilar kayayyaki daga sassan duniya zuwa Koriya Ta Arewa da kuma ɗauko kayayyaki daga Koriya Ta Arewa.

Shugaban kwamitin aiwatar da takunkumin da aka ƙaƙabawa Koriya ta Arewan da aka mai da ita saniyar ware Hugh Griffins, shi ne ya ba da wannan sanarwa jiya a wani taro na manema labarai.

Griffith, ya ce haramta wa jiragen zirga-zirga ya fara aiki ne daga ranar Alhamis ta makon jiya. Kundin bayani kan jiragen ruwa ya nuna jirage da ake kira Petrel 8, da aka yi wa rijista a Comoros, da Hao Fan 6, dake amfani da tutar Saint Kitts da Neɓis, da jirgin ruwan Koriya ta Arewa da ake kira TONG SAN 2, jirgi na huɗu shi ne Jie Shun, ba shi da rijista daga ko wace ƙasa.

A cikin watan Agusta ne kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da wani ƙuduri da ya haramta wa Koriya ta Arewa jigilar gawayin Kwal, da tama da ƙarafa, da kuma abinci daga ruwa zuwa kasuwannin duniya, a zaman martani na nasarar gwajin makami mai linzami da zai iya ratsa nahiyoyi.

Exit mobile version