Bello Hamza" />

Majalisar Birtaniya Za Ta Sake Kada Kuri’a Kan Yarjejeniyar Brexit

A ranar Talata ake saran Majalisar Birtaniya ta sake kada kuri’a kan yarjejeniyar da Firaminista Theresa May ta cimma da kungiyar tarayyar Turai kan shirin ficewar kasar daga EU a ranar 29 ga wannan wata.
Watanni biyu da suka gabata ne Majalisar ta yi watsi da yarjejeniyar ta Theresa may bayan kada kuri’a da rinjayen kuri’y 230, inda Majalisar ta bukaci May ta koma Brussels don sake sabunta yarjejeniyar ficewar tsakaninta da wakilan kasashen Turai.
Sai dai tun a wancan lokaci shugabannin kungiyar ta EU sun ki amincewa da bukatar Theresa May, ko da dai akwai kasashen da ke ganin akwai sauran dama ga Birtaniyar don samar da wasu gyare-gyare a kunshin yarjejeniyar.
Dai dai lokacin da Theresa May ke ci gaba da bin kan shugabannin kungiyar ta EU, gabanin kada kuri’ar a yau Talata, matukar aka gaza samun wani ci gaba gabanin zaman kada kur’ar a yau kai tsaye majalisar za ta sake yin watsi da yarjejeniyar.
Fiye da mako guda kenan, wakilan Birtaniyar da na Kungiyar Tarayyar Turai na tattaunawa da juna don samar da mafita kan batun, inda ko a jiya Theresa May ta yi tattaki zuwa Strasbourg na Faransa a wani yunkuri na samar da mafita kan bukatar birtaniyar ta yi wa yarjejeniyar kwaskwarima.
A ranar 29 ga watan nan ne Birtaniyar a hukumance za ta fice daga kungiyar tarayyar Turan ta EU.

Exit mobile version