Majalisar Dattawa Ga Buhari: Ka Ayyana ‘Yan Bindiga A Matsayin ‘Yan Ta’adda

Daga Sulaiman Ibrahim,

Majalisar Dattawa a ranar Laraba ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Ta kuma shawarci shugaban da ya yi yaki da ‘yan bindigar gaba daya, gami da tayar da bama-bamai a duk wuraren da suke don kawar da su.

Kamar yadda muka sani cewa yan bindigar sun addabi Kaduna, Zamfara, Sokoto, Katsina, da Kebbi a Arewa maso Yamma da Neja a Arewa ta Tsakiya.

Sun kashe dubban mutane, dangi da yawa sun yi hijira sannan kuma sun gurgunta rayuwar zamantakewa da tattalin arziki, duk da matakai daban-daban da gwamnatocin suka dauka don dakile harkokin ‘yan bindigan amma ba su iya haifar da sakamakon da ake bukata ba.

Exit mobile version