Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da harsashen kasafin kudi na 2021 wanda yawansa ya kai naira Tiriliyan N13,588,027,886,175tn.
An samu karin sama da naira biliyan 500 daga kasafin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiko na tiriliyan N13.082,420,568,233tr tun da farko. Hakan kuma ya bada damar cike gibin wasu wuraren da hadakar kwamitocin majalisar wakilai da ta dattawa suka nemi shugaban kasa da ya yi domin tabbatar da gudanar da ayyukan da za su kai ga inganta rayuwar ‘yan kasa da ciyar da kasar gaba.
Amincewa da kasafin ya biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan kasafi ya gabatar na bada shawara kan hakan.
Shugaban kwamitin kasafi na majalisar, Sanata Jibrin Barau, ya mika rahoton nasu a gaban majalisar yayin zamanta na jiya Litinin.
Sannan kuma majalisar ta amince da tiriliyan N4,125,149,354,222 a matsayin kudin gudunmawar da za ta tattara domin gudanar da manyan ayyukan raya kasa.
Da yake nuna farin cikinsa kan amincewa da kasafin da majalisar ta yi, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana cewar a kowani lokaci a shirye suke suke amincewa da kasafin kudi a kan lokaci domin baiwa majalisar zartarwa damar gudanar da ayyukan raya kasa.
Ya kuma ce, ya ji dadin da aka kammala gabatar da kasafin kafin bukukuwan kirisimeti da na sabuwar shekara.
“Bari na fara yi mana murnar yin aiki tukuru wurin ganin mun amince da kasafin 2021 a kan lokaci kafin tafiya hutun Kirsimeti. A shirye muke kowace shekara mu ci gaba da yin ayyukanmu a kan lokaci domin amincewa da kasafin kudi a kan kari domin bada damar gudanar da ayyukan da aka tsara na raya kasa,” a cewar shi.