Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da kasafin kudin shekarar 2021 a zamanta na musamman yau Litinin. Majaliar ta amince da Naira tiriliyan 5.6 a matsayin kudin ayyukan yau da kullum da tiriliyan 4.1 na manyan ayyuka da tiriliyan 3.3 na biyan bashi.
Kazalika, an ware naira tiriliyan 4.1 a matsayin kudaden da za a tattara domin gudanar da manyan ayyuka. Jimilla, majalisar ta amince da kudi Naira tiriliyan 13.5, karin biliyan biyar kenan a kan wanda Shugaba Buhari ya gabatar mata a watan Oktoba na tiriliyan 13.
Bayan kammala yi wa kasafin karatu na uku a yau, Shugaban Majalisar Ahmad Lawan ya nuna jin dadinsa kan yadda suka amince da kasafin kafin tafiya hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.
“Bari na fara yi mana murnar yin aiki tukuru wurin ganin mun amince da kasafin 2021 a kan lokaci kafin tafiya hutun Kirsimeti,” in ji shi.