Majalisar Dattawa Ta Umurci Kwastam Ta Maida Wa ‘Yan Kasuwa Kayansu A Oyo  

Majalisar Wakilai

Daga Abubakar Abba

Kwamitin da’a da karbar koke na Majalisar Dattawa ya umarci Hukumar Hana Fasa kwauri ta kasa  da ta mai do da kayan da  jami’anta suka  kwace  a yayin da suka kai farmaki a kan wasu shaguna da ‘yan kasuwa suka jibge buhunan shinkafa a garin  Ibadan da ke a cikin jihar  Oyo.

Shugaban kwamitin  Sanata  Ayo Akinyelure ne ya bayyana hakan bayan zaman Da kwamitinsa ya yi kan sa koken ‘yan kaauwar da ke da shagunan na Shinkafar.

‘Yan kaauwar sun gabatar da koken na su ne ta hanyar Sanata Kola Balogun,  mai wakiltar mazabar  Oyo  ta Kudu,  inda ‘yan kasuwar a cikin takadar su ta Koken suka yi zargin cewa,  Jami’an na Kwastam,  sun kai samame a kasuwannin  Oja Oba  da Bodija  da ke duk a garin  Ibadan, inda suka kwace kayan miliyoyin naira.

Sanata  Akinyelure ya yi kira ga Kwantirola Janar na Kwastam na kasa Hameed Ali  wanda mataimakin Kwantirola Janar Garba Mohammmed ya wakilta da su maido da kayan da suka kwace ga ‘yan kasuwar a tsakin sati biyu tare da bude masu shagunan su da kuma maido da kudaden da suka dauka daga cikin shagunan ‘yan kasuwar.

Da yake mayar da martani mataimakin Kwantirola Janar  ya bayyana cewa,  sashe na 147 na dokar aikin hukumar Kwastam ta ba mu karfi kamar yadda aka bai wa ‘yan sanda karfin gudanar da bincike a cikin haraba a ake zargin an jibge haramtattun kaya a cikin dare ko da rana.

A cewar  Kwantirola  Garba Mohammmed ya Ya bayyana cewa, “Muna da ‘yancin fasa tagogi ko shagunan bisa hujjojin da muke da su”,  inda ya kara da cewa,  an kwace kayan ne bisa wasu bayanan sirri da hukumar ta samu.

Ya bayyana cewa, “Ba mu da nufin cire mutane daga cikin kasuwancin su domin shugabanmu na kasa mutum ne mai son ganin ana bin ka’ida.

Akna maganar  na Jihar Katsina, ya ce,  “Ban san komai a kai ba,  inda ya kara da cewa,  in har shinkafar kasar waje ce,  ina kokwanton ba za a dawo da ita ba”.

Exit mobile version