Majalisar Dattawa Ta Yi Tir Da Karancin Fasfo

A jiya ne Majalisar Dattawa ta yi allawadai da wahalar da ‘yan Nijeriya ke sha wajen neman fasfo, musamman ga masu aniyar fita wajen kasarnan. Daganan sai majalisar ta umurci Hukumar shige da fice, ‘Immigration’ da ta yi duk abin da ya wajaba ta yi domin magance matsalar ta karancin fasfo din.

Shugaban Majalisar Dattawan ne, Bukola Saraki, ya bayar da wannan umurnin a lokacin da yake bude ofishin bayar da fasfo din a ginin majalisar da ke Abuja. Amma dai ya yabawa Konturolan Hukumar ta shigi da fici, Muhammad Babandede,  a kan hobbasan da ya yi na bude ofishin karban fasfo din a zauren majalisar.

A cewar Bukola Sarakin, sam hakan ba daidai ne ba, a ce mutum ya nemi fasfo din amma sai ya kwashe kwanaki yana jira kafin ya kai ga samu. Ina kuma fatan Kwanturolan hukumar zai yi duk hikimar da zai iya domin ganin wannan matsalar ta karancin fasfo ta kau.”

“Na yi tafiya kasashe masu yawa, kuma duk koken da nake samu iri guda ne na karanci gami da wahalar samun katin fasfo din.”

Sai dai Saraki, ya kara nanata jinjinawa hukumar kan bude ofishin karban fasfo din a zauren Majalisar, inda ya tabbatar da hakan zai kara dankon zumunta a tsakanin Majalisar da sashen gwamnati.

Exit mobile version