Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya Sanata Ahmad Lawan, ya shaida cewar majalisar ta kimtsa domin gudanar da zama na musamman kan kasafin 2021 tare da amincewa shi a ranar Litinin mai zuwa.
Lawan ya shaida hakan ne a yayin zaman majalisar a jiya biyo bayan kudurin da Sanata Yahaya Abdullahi (APC daga mazabar Kebbi ta arewa) ya gabatar, da ya samu marawar bayan shugaban marasa rinjaye Enyinnaya Abaribe (PDP daga mazabar Abia ta kudu).
A cewar shugaban majalisar, jinkirin amincewa da kasafin ma da aka samu tun da fari, ya biyo bayan bukatar da kwamitin majalisar kan kasafi ya yi wa gwamnati na kara yawan kudade.
“Kwamitinmu kan kasafi ya dukufa gudanar da aiki babu dare ba rana. Mun tsara amsar rahoto daga kwamitinmu kan kasafi a yau (jiya kenan) amma a sakamakon jinkirin bukatar karin kudi daga suka yi daga wajen gwamnati, muna son ne kwamitinmu ya tabbatar ya yi aiki da ababen da suka dace da kamata.
“Wannan yana sake bayyana irin yadda majalisar take da zimmar amincewa da kasafi a kan lokaci, mun yin hakan a shekarar da ta gabata, da yardar Allah za mu cigaba da yin hakan,” inji Lawan.