Majalisar Dattijai Ta Bukaci CBN Da NDIC Su Ilimantar Da ’Yan Nijeriya A kan Hatsarin Bit-coin

Majalisar dattijai ta bukaci Hukumar Babban Bankin Niijeriya CBN da ta ilimantar da ‘yan Nijeriya illar da ke tattare da tsarin zuba jari na Bitcoin, sun ce ya kamata a sanar da jama’a a manyan yarukan kasar nan da muke dasu domin yada wa ga ‘yan Nijeriya.

Majalisar ta kuma bukaci hukumar wayar da kan ‘yan Nijeriya ta NOA da ta yada hadurran dake tattare da tsari damfaran nan na bankunan da ke yin alkawuran kudaden da suka wuce tunani suke kuma gudanar da aiyukansu a kasarnan.

Sun kuma bukaci kwamitin Bankuna na kasa da sauran cibiyo yin hada-hadar kudade na kaaar nan dasu binciki tsarin zuba jari na Bitcoin su kuma dawo mata da rahoto cikin mako biyu.

Wannan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Sanata Benjamin Uwajumogu (APC-IMO) ya mikawa majalisa ne in da ya nuna damuwarsa a kan karuwar tsarin zuba jari na damfara irin na Bitcoin da sauransu a fadin kasar nan.

“Wannan tsarin na nan ana tallarsa a kafafen watsa labarai ga ‘yan Nijeriyar da basu san hatsarin dake tattare da shi ba, a na bai wa ‘yan Nijeriya shawarwarin fada wa tsarin da alkawarin ninka musu ribar su cikin dan kankanin lokaci” in ji shi.

Sanata Uwajumogu ya kara da cewa, wani shahararren masani tattalin arziki JP Morgan, ya fada a wani taro da aka yi a garin New York ta Amurka cewa, harkar Bitcoin, harka ne da ta yi dai-dai da ta masu safarar kwayoyi kuma cikin kankanin lokaci zai rushe. Ya tunatar da yadda harkar MMM ta jefa ‘yan Nijeriya cikin halin kakanakayi inda suka yi asarar Miliyoyin Nairori a shekarar 2016.

A nasa gudumawar Sanata Dino Melaye ya ce hakin gwamnati ne kare ‘yankasa daga ‘yan danfara masu yawo da tsarin zuba jari na bogi. Ya bukaci hukumar NOA su fadakar da ‘yan Nijeriya a kan bukatar yin hattara wajen fadawa harkar ‘yan danfara. Matamakin shugaban majalisar dattijai Mista Ike Ekweremadu ya karfafa mahimmanci bukatar Hukumar NOA su shirya gangamin fadakar da ‘yan Nijeriya a kan hadarin wannan tsarin zuba jarin.

 

Exit mobile version