Majalisar Dinkin Duniya Ta Kadu Da Mutuwar ‘Yan Gudun Hijira 35 Sakamakon Korona

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna kaduwarta game da mutuwar ‘yan gudun hijira 35 sakamakon kamuwa da cutar Korona a sansaninsu da ke Maiduguri.

Babban Jami’in Kula da Ayyukan Majalisar Dinkin Duniya a Tarayyar Nijeriya, Mista Edward Kallon ya bayyana haka a wata ziyara da ya kai wuraren kwantar da ‘yan gudun hijira da suka kamu da cutar Korona a Maiduguri da ke Jihar Borno.

A sakamakon abin da suka gane wa idonsu yayin ziyarar, ya ce majalisar za ta taimaka wa sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jihar Borno da kayayakin yaki da Annobar cutar ta Korona.

Ya kara da cewa a bisa hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayyar da Majalisar Dinkin Duniya da Gwamnatin Jihar Borno za su tabbatar da an kara yawan tallafin kayan yaki da cutar a dukkanin sansanonin da ke Maiduguri.

Ya ce yin amfani da magunguna da abubuwan kariya daga yaduwar cutar kamar abubuwan rufe fuska da baki da ruwan wanke hannaye da sinadaren kashe kwayoyin cuta da ake shafawa a hannaye zai taimaka wa mazauna sansanonin.

Sannan duk wani mai ta’amali da shiga sansanonin a samar da kayayakin agaji na kariya gare shi saboda dakile yaduwar annobar cutar ta Koronabairus a guraren da kuma kauyukan da al’umman karkara ke rayuwa a gurin.

Ya kara da cewa sun ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijira kuma sun ga guraren da aka kebe domin kula da yaki da annobar cutar a yankin Maiduguri.

Ya ce, Majalisar tana yaba wa jami’an kiwon lafiya nata da kuma abokan aikinsu na kungiyar Likitocin Nijeriya da ma jihar Borno da ke aikin samar da agajin kiwon lafiya a sansanin.

Ya ce tun lokacin da cutar ta yi kamari aka fara samun yaduwarta a sansanin ‘yan gudun hijira inda Gwamnatin tarayya da Majalisar Dinkin Duniya suka kara tura malaman kiwon lafiya na masamman da za su shawo kan matsalolin yaduwar cutar.

Exit mobile version