Umar A Hunkuyi, " />

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yaba Da Tallafin Ciyarwa Ga ‘Yan Gudun Hijira

Majalisar Dinkin Duniya ta yaba wa Madam Sharu Lada, dangane da taimaka wa al’ummar yankin ta wadanda suke gudanar da rayuwar su a sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Borno.
Mutanen kauyen Doro da ke jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Nijeriya, suna gudanar da rayuwar su cikin kunci da matsuwa a sansanin ‘yan gudun hijira tun bayan da hare-haren ta’addanci na kungiyar Boko Haram da ya addabi al’ummar yankunan.
Majalisar Dinkin Duniya, ta yaba da irin kokarin da Madam Sharu Lada ke yi wajen kulawa da rayuwar al’ummar yankin ta. Ta yadda ta ke taimaka masu da abubuwan abinci da na kashewa. Kimanin shekaru goma al’ummar kauyen Doro suke gudanar da rayuwarsu a sansanin gudun hijira ita kuma tana waiwayar su tana taimaka masu.
An yaba da yadda rayuwar Madam Sharu da maigidanta ke gudana saboda ba su manta da ‘yan’uwan su ba. Lada tare da maigidanta suna da yara biyar amma suna kokari wajen tunawa da dangi da sauran al’umma. Mazauna kauyen Doro sun rasa gidajensu da abubuwan da suke gudanar da rayuwa a kauyen su sakamakon hare haren da ‘yan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka rika kai masu.

Exit mobile version