Majalisar Dinkin Duniya Ta Yaba Wa Buhari Kan Riga-kafin Korona A Nijeriya

Majalisar

Dr Ngong Cyprian receives his first dose of the Oxford/AstraZeneca coronavirus disease (COVID-19) vaccine from Dr Faisal Shuaib, Executive Director and Chief Executive Officer of the National Primary Health Care Development Agency, at the National hospital in Abuja, Nigeria, March 5, 2021. REUTERS/Afolabi Sotunde

Daga Zubairu M. Lawal,

Babbar Darakta a ofishin Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Misis Winnie Bynanyima ta yaba wa Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari saboda saurin ba da maganin allurar Riga-kafin Annobar cutar korona a cikin kasarsa.

Tace; Shugaban Kasar Nijeriya yana cikin jerin Shugabannin Kasashe da suka bada kulawa wajen yaki da yaduwar Annobar cutar.

Kuma Shugaban na Nijeriya ba bata lokaci ba wajen tabbatar da ganin maganin Rigakafin ya fara aiki a kasarsa cikin lokaci.

Bayan gudanar da Aluran ga Shugaban kasan tuni aka cigaba da gudanar da aluran zuwa jihohi domin dakile yaduwar Annobar cutar korona.

Misis Winnie  Bynanyima Tayi kira da ayi adalci wajen rabon maganin Rigakafin Koronan kuma a tattabatar kasashen da basu da karfi suma ba a barsu a baya ba wajen dakile yaduwar wannan Annobar ta  cutar korona.

Daraktan ta kara da cewa a yayin da ya kaiwa Shugaba Buhari ziyara na musamman a dakin taro na state house dake Abuja.

Misis Byanyima ta ziyarci wajen taronne  a watan maris  8-10, shine ziyararta na farko tunda aka bata mukamin a shekarar 2019. Najeriya ta soma yiwa ma’aikatan lafiya Rigakafinne tun 5 ga watan maris bayan an kawo maganin Rigakafin kusan na miliyan hudu.

Wanda ya  biyo ta hannun wata kungiya mai suna COBAD. Ita wannan kungiya sune suka dauki alhakin raba maganin a fadin duniya baki daya.

A yayin ganawarta da Shugaba Buhari, Misis Byanyima tayi bayani kan yadda Kasar Najeriya tayi kokari wajen ganin an dakile yaduwar cutar HIB da kuma na Kobid-19.

Ziyararta tana daga cikin kwana uku na ran gadin da zatayi a fadin kasar zuwa wurare da dama domin ganin yadda ake bada Rigakafin,

Exit mobile version