Muhammad Maitela" />

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tir Da Harin Sansanin ‘Yan Gudun  Hijira A Barno

Babban ko’odinatan Majalisar dinkin duniya a Nijeriya, Mista Edward Kallon, ya yi tofin Allah- tsine dangane da harin da aka kai a matsugunin yan gudun hijira, da ke kauyen Dalori- kusa da birnin Maidugurin jihar Barno.

Matsugunin, wanda ya kunshi ‘yan hijira sama da mutum 12,600, da ke zaman Allah ya ba-ku- mu-samu wadanda rikicin Boko Haram ya tagayyara, a yankin Arewa maso-gabashin Nijeriya.

Gamayyar ‘yan bindigar, wadanda da suka kai farmaki a sansanin, a cikin duhun dare a kauyen Dalori hadi da kauyuka hudu da ke kusa da shi, ya jawo mutuwar akalla mutane takwas (8) inda da dama kuma sun samu raunuka, tare da yin garkuwa da mata a yankin- baya ga kona kauyukan da yin awon gaba da kayan abinci.

Bugu da kari kuma, lamarin da ya tilasta daruruwan jama’a tserewa daga yankin, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA).

“Ina baiwa gwamnatin Nijeriya shawara kan ta dauki matakin kare rayukan jama’a daga fuskantar barazanar a rayukan su “. Inji Mista Kallon.

“Kai hari a matsugunan ‘yan gudun hijira, wanda babbar barazana ce ga rayuwar mata, yara da tsofaffi wadanda matsalar tsaro ta tilasta musu kaurace wa yankunan su. Muna mika sakon jajen mu ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su, da fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka”.

“Wannan hari da aka kai a daya daga cikin wadannan matsugunan yan gudun hijira da ke Dalori; sansani ne wanda aka kafa shi tun a cikin shekarar 2015, wanda ya kunshi mutane 47,500”.

“A watan Junairun 2016, wasu mahara sun taba kai hari a sansanin yan gudun hijirar da ke kauyen Dalori, inda sama da mutum 100 tare da kona kauyen kurmus”. Ya nanata.

“Matsalar ayyukan jinkai a Arewa maso-gabashin Nijeriya, wadda ta hada har da zirin tafkin Chadi- yanzu ta na daya daga cikin manyan kalubale a duniya, inda mutum miliyan 7.7 suna matukar bukatar tallafin gaggawa a wannan shekara ta 2018, a jihohin da matsalar ta fi shafa, a Borno, Adamawa da Yobe, yayin da kimanin mutum miliyan 6.1 suka ci gajiyar agajin”.

“Tun bayan barkewar rikicin, a shekarar 2009, an kiyasta cewa sama da mutum  27,000 ne suka rasa rayukan su, a wadannan jihohi guda uku, tare da yin garkuwa da dubban mata da yara kanan, da amfani dasu a wasu hare-haren kunar bakin wake”. In ji Kellon.

 

Exit mobile version