Bello Hamza" />

Majalisar Dinkin Duniya Tayi Tir Da Harin Birnin Gwari

Daga Bello Hamza

 

Sakataren majalisar dinkin duniya (UN), Mista António Guterres, ya yi Allah wadai da hare haren da aka kai yankin Birnin-Gwari ta jihar Kaduna inda mutane da dama suka rasa rayukansu wasu kuma da dama suka jikkata yayin da dukiyoyi na dimbin naira suka salwanta.

Mista Guterres, ya bayyana haka a wata sanarwa ta hanun jami’in watsa labaransa mai suna, Stephane Dujarric, ya kuma kara da cewa, a kwai bukatar hukunta duk wabni mai hannu a wadaan kashe kashen da aka yi.

Kafafen watsa labarai sun ruwaito cewar, akalla mutum 70 ciki har da kananna yara aka kashe ranar Asabar a kauyen Gwaska dake karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

“Dole a gaggauta hukunta duk mai hannu a cikin wannan danye aikin” inji shi.

Guterres ya kuma nuna takaicin sa a bisa ci gaba aukuwar tashe tashen hankula a yankin, saboda haka ya nemi a masu ruwa da tsaki su hada hannu wajen ganin an samar da zaman lafiya a yankin dama kasar baki daya.

Majalisar dinkin duniyar ta kuma mika ta’aziyar ta ga iyalan wadanda suka rasu da gwamnatin Nijeriya gaba daya tare da addua’ar Allah ya gaggauga ba wadanda suka samu raunuka sauki.

A watan Afrilu masu hakan ma’adanai 14 ne aka bayar da labarin irin wannan al’amarin ya faru dasu.

Mista Guterres ya kuma lura da cewar, Nijeriya ta dade tana fuskantar rikicin ‘yan ta’addan Boko Haram, yakin daya ci yawukan mutane da dama da kuma tarwatsa wasu dubbai daga muhallinsu.

 

 

Exit mobile version