Khalid Idris Doya" />

Majalisar Dokokin Bauchi Ta Soke Dokar Kwato Dukiya Daga Barayin Gwamnati

A ranar Laraba ce Mambobin Majalisar Dokokin jihar Bauchi suka amince da kudurin dokar da ya dakatar da kwato kudade da kadarorin jama’an jihar da aka yi sama-da-fadi da su wadda aka kafa a shekarar 2017.
Baya ga wannan kuma, majalisar ta kuma amince da kudurin karin sabbin Hakimai, Masu Gundumomi da masu Unguwanni a fadin jihar.
‘Yan majalisa 13 daga cikin ‘yan majalisa 31 da Bauchi ke da su ne suka gabatar da kudurin, kana suka kuma amince da shi a tsakaninsu.
Kudirin karin Hakimai, Masu Unguwanni da Dakatai gami kuma da soke dokar kwato kudade da kadarorin jama’a da wasu suka wawushe, mataimakin masu rinjiye a majalisar, Honorabul Abdullahi Abdulkadir wanda shi ke wakiltar mazabar Bura shi ne ya gabatar da kudurin, wadda ya samu mara baya daga dan majalisa Sale Nabayi da ke wakiltar Ganjuwa ta Yamma da Magaji Inuwa da ke wakiltar mazabar Jama’are a cikin majalisar.
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Kawuwa Shehu Damina ya baje kudurin a gaban majalisar domin tafka muhawara a tsakanin ‘yan majalisar jihar, wanda ya shiga karatu na biyu da na uku ba tare da wani kin amincewa ba daga cikin ‘yan majalisu 13 da suka halarci zaman majalisar daga cikin mambobi 31 da majalisar ke da su.
Kakakin ya kuma nuna cewar za su nemi ra’ayin jama’ar jihar kan wannan sabuwar dokar hadi da tabbatar da cewar majalisar jihar ta bi dukkanin hanyoyin da suka dace wajen ganin gwamna ya sanya hannu don amincewa da wannan dokar domin ta fara aiki.
Mista Damina ya roki gwamnan jihar ya gaggauta sanya hannu kan wannan dokar domin tabbatar da shi a matsayin wanda ya zama doka.
Sai dai kuma, a wani martani da kakkausar murya, Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Lere/Bura a majalisar, Hon. Aminu Tukur ya shaida cewa kudirin dokar an gabatar da ne bisa son rai na wasu daidaiku. Ya kuma ce wannan cin amanar jama’ar jihar ne, inda ya shaida cewar jama’an jihar Bauchi ba za su taba yafe wa Kakakin majalisar kan wannan matakin nasa ba.
Ya ce, abin mamaki ne ma majalisar ta kira mutane 13 zama a asirce maimakon mambobi 31 da suke da alhakin kan zaman, ya kuma ce sun saba bude zaman majalisar ne da karfe 10 na duk ranar da za su yi zama, amma a wannan ranar ta Laraba sai aka fara zaman da karfe tara 9 na safe domin wadanda ake so su kasance su kadai ne suka shiga zaman.
“Mambobi 13 da suke da ra’ayin gwamna mai barin gado su ne suka shiga suka yi rawarsu da kidarsu, daman suna da tsarinsu. An yi dokar ne domin dukkanin wadanda ya karkatar da dukiyar jama’a ya maido da su, amma da yake shi gwamna ya gaza samun nasarar zarcewa a karo na biyu don haka ne ‘yan majalisar da suke tare da shi suka halarci majalisar da karfe 9 na ranar Laraba domin sauya dokar.”
Ya ce, an soke wancan dokar ce kawai domin gwamnan ya samu damar da ba za a bincike shi ba, wanda ya nuna cewar jama’ar jihar sam ba za su taba maraba da wannan matakin ba.

Exit mobile version