Connect with us

RAHOTANNI

Majalisar Dokokin Borno Ta Yi Rashin Mambanta Daya

Published

on

Allah ya yi wa dan majalisar dokokin jihar Borno rasuwa, Hon. Wakil Bukar rasuwa, wanda shi ne dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Ngazai a zauren majalisar.

Hon. Wakil ya rasu ne a ranar Talata, bayan gajeruwar rashin lafiya, wadda ba a bayyana ba.

An haufi Hon. Bukar a shekarar 1964 a kauyen Gadai da ke karamar hukumar Ngazai da ke jihar Borno. Ya yi karatun sa cibiyar NTI a garin Gajiganna, wanda daga bisani kuma ya zarce jami’ar Maiduguri.

Haka kuma, an sha zabar marigayin matsayin kansila a lokuta daban-daban, kuma a karkashin jam’iyyu, SDP, PDP, dan takara mai zaman kansa a yankin sa.

Har wala yau kuma, ya samu nasarar kasancewa zababben dan majalisar dokokin karamar hukumar sa tun daga shekarar 2007 zuwa lokacin rasuwar sa. Kuma ya rasu ya bar mata da yaya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: