Daga Ibrahim Muhammad Kano,
A kokarin da majalisar Dattijan kasarnan take na yaki da miyagun kwayoyi da har ta yi hadin gwiwa da majalisar dokokin Jihar Kano don bijiro da dokokin da yakamata, da zai taimakawa maganta matsalar shaye-shayen a Kano da sauran sassan kasarnan tasa babban mataimaki ga mataimakin shugaban majalisar Dattawa Omo Agege,Kkma ko’odineta na yaki da shaye-shaye a ofishinsa Hon. Injiniya Musa Mujahid Zaitawa ya ziyarci sabon shugaban majalisar dokokin jihar Kano Injiniya Ibrahim Chidari a majalisar Kano.
Da yake bayyana makasudin ziyarar Injiniya Musa Mujahid Zaitawa ya ce, ya ziyarci kakakin majalisar Kanon ne akan taya shi murna kan wannan matsayin da Allah ya bashi na jagorancin majalisar Kano.
Ya ce, sannan kuma a baya kafin zuwan sabon shugaban majalisar ya taba zuwa ya zauna da ‘yan majalisar jihar ta Kano wanda aka sami wakilcin wasu ‘yan majalisun daya daukesu zuwa wajen mataimakin shugaban majalisar dattijai na kasa, akan yanda ake yaki da shaye-shaye da matsalar fyade.
Ya kara da cewa yanzu kalubalen da yake gabansu shi ne matsalar yawaitar shaye-shaye kuma Kano ita ce jihar da a Arewa tafi munin yawan masu harkar shaye-shaye shi yasa yazo neman hadin-kan majalisar Kanon dan hada hannu wajen maganta wannan matsalar.
A nasa jawabin Kakakin Majalisar dokokin Rt. Hon. Injiniya Ibrahim Chidari ya bayyana mutukar godiyarsa bisa ziyarar da mataimakin na musamman ga mataimakin shugaban majalisar Dattawa Injiniya Musa Mujahid ya kawo majalisar Kano.
Ya ce, bayyanai da ko’odinetan yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi a ofishin mataimakin shugaban majalisar Dattawan ya yi bayanai ne masu muhimmanci na yaki da wannan mummunar halayya da suka addabi al’umma musamman matasa anan jihar Kano da kasa Baki daya. Kuma majalisar Dattawa ta riga ta dauki mataki na tabbatar da dokoki da dukkanin hanyoyi da za a tabbatar da kauda wannan matsalar da ta addabi al’umma dan shawo kanta.
Rt. Ibrahim Chidari ya yi alkawarin cewa majalisar dokokin jihar Kano duk abinda ya tasi nayin doka kona bayar da gudummuwa za su bada goyon baya da hadin-kai don tabbatar da nasarar yaki da shan miyagun kwayoyi.