Daga Sagir Abubakar, Katsina
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta bukaci bangaren zantarwar jihar da ya gyara hanyar burji da ta tashi daga gangaren Makurdi zuwa Jargaba Unguwar Daga zuwa Gidan Kanawa har zuwa Unguwar danbaushe Kanadarawa a yankin karamar hukumar Bakori.
Wannan ya biyo bayan wani kuduri da dan majalisa mai wakiltar yankin, Dr. Ibrahim Aminu Kurami ya gabatar a zauren majalisar.
Kamar yadda dan majalisar y ace idan aka gyara hanyar za’a bunkasa tsaro da kuma ba al’ummonin yankin damar samun sauki wurin kai kayayyakin amfanin gonarsu zuwa kasuwanni.
Haka kuma, dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Batagarwa Tukur Iliyasu Shagumba ya gabatar da wani kudurin dake yin kira ga bangaren zartaswa da ya gina hanyar burji daga marken magaji dan-iyau-sha-iri-Ajiwa.
Da yake kare kudurin, dan majalisar ya ce ta hada al’ummoni da dama dadin dadawa zata taimaka wmasu wajen raga masu wahalhalun daukar kayayyakin amfanin gona zuwa kasuwanni.
Kazalika, dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Charanchi Lawal isa Kuraye ya gabatar da wani kuduri dake bukatar bangaraen zartaswa ya gina karin ajujuwa da kuma katange makarantar sakandiren gwamnat ta Charanchi.
Bayan tafka muhawara akan kudurin guda biyu (2), shugaban majalisar Tasi’u Musa Maigari ya umarci akwaun majalisar da ya gabatar da matsayar damajalisar ta cimmawa domin aiwatarwa.