Connect with us

LABARAI

Majalisar Dokokin Katsina Za Ta Binciki Mahdi Shehu

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Katsinna za ta binciki zargin yin almundahana da sama da fadi da wani dan kasuwa mazaunin Kaduna mai suna, Alhaji Mahadi Shehu, ya yi wa gwamnatin Jihar.

Sakataren gwamnatin Jihar ta Katsina, Dakta Mustapha Mohammed Inuwa, ne ya yi nu ni da hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani shirin gidan Rediyon Nijeriya da aka saurara a Katsina.
Ya ce, “Dukkanmu ‘yan adam ne, don haka muna iya yin kuskure. In har kana da matsala da gwamnati, to ka nemi bayani ne daga gareta amma ba sai ka shiga kafafen yada labarai kana ta soki-burutsu ba.
“Gwamnatin Jiha ta bai wa majalisar Dokokin Jiha damar ta binciki dukkanin zarge-zargen da Mahadi Shehu yay i, ta kuma gayyaci duk wanda take so ba tare da an yi mata katsalandan ba.
“A iyaka sani na, babu wata rashin fahimta a tsakani na da Mahadi, na kuma san an dan jima ba mu sadu da juna ni da shi ba, hakanan shi ma Gwamna ya shaida mani cewa ya ma yi aiki tare da yayansa a hukumar ruwa, babu kuma wani sabani da ya faru da har zai sabbaba irin wannan babatun da yake ta yi.
“Mun ma yi wani ciniki tare da shi a kwanan nan, a lokacin da ya aiko mani da wasu kwayoyin magani. Sam ni ba ni da wani sabani da shi, sam-sam, hakan shi ma Gwamna.
“Amma dai kamar yanda ka fada ne, akwai alamun siyasa ce a mahangar zaben shekarar 2023. Akwai mutanan da suke ta kwadayin kujerar gwamna. Don haka suke ganin in har ba su kawo wata ‘yar hatsaniya ko sukar wani ba, da suke zatonsu su ka kare masu gaba, hakarsu ba za ta tarar da ruwa ba.”
A kan batun rashin tsaro, Sakataren gwamnatin ya yi nuni da cewa akwai wasu mutanen da su ke da sha’awar ci gaba da nu na gazawar wannan gwamnatin don kawai su ce ta gaza samar da tsaro a wajen yakin neman zabensu.
Abduljalah Runka, shugaban kwamitin majalisar Dokokin ta Jihar Katsina, ya shaida wa sashen Hausa na gidan Rediyon BBC a shirinsu da aka saurara a Katsina cewa, Majalisar Dokokin ta ma fara gudanar da binciken maganar domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Advertisement

labarai