Daga Sharfaddeen Sidi Umar,
Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta aminta da Kasafin Kudin 2021 na naira biliyan 176.7 domin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya rattaba hannu.
Wannan ya biyo bayan amincewa da rahoton Kwamitin Kudi da Kasafin Kudi a zaman Majalisar wadda tun da farko Gwamna Tambuwal ya gabatar mata da daftarin Kasafin Kudi a ranar 15 ga Disamba.
Kasafin Kudin wanda ke da taken “Kasafin Tattaro Muhimman Ayyuka da Bunkasa Tattalin Arziki da Walwalar Jama’a” fannin ilimi ne ya samu kaso mai yawa, sai aikin gona da kiyon lafiya da suka samu kaso na biyu da na uku. A zaman Majalisar na jiya ne kasafin ya samu karatu na biyu a gaban Majalisar.
“A bisa ga bukatoci masu muhimmanci daga kananan kwamitoci, kwamitin ya karkatar da wasu kudade domin biyan wasu muhimman bukatocin al’umma,” in ji Hon. Basakkwace.
Shugaban Kwamitin ya ce kashi 54 na Kasafin Kudin zai tafi ne ga manyan ayyuka, a yayin da al’amurran yau da kullum suka samu kashi 46 na bakidaya Kasafin Kudin na 2021 wanda ya bayyana cewar zai samar da ci-gaba mai ma’ana ga al’ummar Jihar Sakkwato.