Majalisar dokokin kasar Uganda ta dakatar da muhawara kan daftarin dokar da ke neman bawa Yuweri Musebeni damar sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa.
Shugaban majalisar dokokin kasar Jacob Oulanyah, shi ne ya sanar da dakatar yin mahawarar a lokacin da yake gabatar da jawabi ga sauran ‘yan majalisar kasar a birnin Kampala, inda ya ce an yi hakan ne domin kwantar da hankula.
Oulanyah, ya ce akwai yiyuwar za a sake dawo da wannan batu domin ci gaba da mahawara a zauren majalisar a wata ranar da bai bayyana ba a nan gaba.
Masu fafutukar kare dimokuradiyya, shugabannin addinai da kuma ‘yan siyasa cikin har da wadanda ga al’ada suka saba goyon bayan Musebeni da dama ne ke nuna adawa da yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara don bai wa shugaban damar sake tsayawa takara a zaben da za a yi a shekara ta 2021 idan Allah ya kai mu.