Majalisar Jigawa Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Tsige Gwamna Badaru

Daga  Idris Aliyu Daudawa

Shugaban makarantar bunƙasa ci gaban fasaha AFIT wadda ke ƙarƙashin Rundunar Sojojin sama ta ƙasa, Isiyaka Bukar, mai muƙamin Iya Ɓice Marshal ne ya bayyana cewa, nan bada jima wa bane makarantar za ta fara ƙera wasu sassan jirgin sama. Wannan niyya kamar yadda ya ce, an ɗauki matakin ne saboda samar da kayayyakin da  Hukumar  Sojojin sama suke buƙata.

Mista Bukar ya yi kira da majalisar ƙasa da cewar ta yi ƙoƙari wajen amincewa da dokar kafata, ko ta samu damar aiwatar da ayyukanta kamar yadda ya dace.Ya ƙara da cewar ‘’ Idan  aka amince da ƙudurin da zai zama doka, zai ba ita cibiyar wata dama ta wasu kayayyaki da kuma taimakawa gwamnatin tarayya, a ƙoƙarin da take na samar na ganin tana samu da wasu kayayyaki da suke buƙatunta ne, ba sai an je ƙasashen waje ba. Ya furta haka ne a wata ganawa da aka yi da shi a Kaduna.

Ya ce ƙudurin nasu da ake son ya zama doka idan ya samu amincewar majalisar ƙasa, ya haɗu da matsaloli ne , a shekarun da suka gabata. Ya kuma yi kira da ‘yam majalisar ƙasa da suke cikin wa’adinsu,  da cewar, su kafa tarihi wajen amincewa da dokar ƙafa ita cibiyar. Tun lokacin da aka kafa ta zuwa yanzu, cibiyar da yaye ɗalibai 5,680.

Kwamandan ya ƙara jaddda cewar idan aka amince da dokar kafa ita cibiyar, abin zai taimaka wajen matsalolin da take fuskanta waɗanda suka haɗa da, rashin isassun kuɗaɗe, ta ɗauki malamai, sai kuma kayayyakain da zasu taimaka mata musamman tafiyar da harkokin bincike bincikenta.

Bukar ya ce cibiyar na gudanar da kwasa kwasai waɗanda suka haɗa da gyaran jirgin sama, lasisin tuƙin jirgin sama, na cibiyar harkokin jiragen sama ta ƙasa.

Ya nuna jin daɗinsa akan ƙoƙarin da rundunar sojojin jirgin sama take yi a shekarun da suka wuce, ya ci gaba da cewar, ‘’Tun lokacin da wannan gwamnati mai ci ta hau kan gado, suna samun kuɗaɗe daga wurinta, duk da matsin tattalin arzikin ake ciki, gaskiya su abin da zasu ce sai godiya ga Allah’’.

Ya bada tabbacin zasu ci gaba da taimawa ƙasa wajen ƙirƙirƙr wasu kayayyaki waɗanda zasu taimaka, da kuma hanawa a riƙa dogaro da na waje, ko shakka babu cibiyar za ta ci gaba da yin abubuwan da ta saba. Ya ce bukin yaye ɗalibai da ya gabata Ministan zurga zurga  na ƙasa ya samu halarta, sun nuna bajintar su ɗaliban cibiyar, ta wannan hanya ce ita Rundunar sojojin sama ta ƙasa ta amince da ɗaya daga cikin ayyukan ɗaliban da suka kammmala samun horarwa na cibiyar wanda kuma zai amfani ƙasa.

‘’Muna goyon bayanƙoƙari da gwamnatin tarayya ta ken a samar da wasu kayayyakin da muke buƙata, ita cibiya ta taimaka wajen samar da shi, da kuma ita uwa maibada mama Rundunar sojojin sama ta ƙasa.’’

Kamar yadda ya furta da bakinsa ‘’Wannan cibiyar tana samar da abubuwan da suke taimaka mata, cikin gida’’. Cibiyar tana samar da abubuwar da ita Rundunar sojojin sama su ke buƙata’

 

Exit mobile version