Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Majalisar Jigawa Ta Amince Da Hukuncin Kisa Ga Masu Fyaden Da Ke Da Kanjamau … Daurin rai-da-rai ga wadanda ba su da cutar

by Muhammad
February 19, 2021
in LABARAI
2 min read
Hukuncin Kisa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Mahdi M. Muhammad,

Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta amince da hukuncin kisa ga masu aikata fyade da ke dauke da cutar kanjamau mai karya garkuwa jiki matukar an gwada wacce suka yi wa fyaden aka ga ta kamu.

Wannan wani bangare ne na kudirin dokar da majalisar ta gabatar don dakile cin zarafin mutane.

Kakakin majalisar, Honarabul Idris Garba Jahun ne ya sanar da wannan a zaman da suka yi a ranar Larabar da ta gabata.

Honarabul Abubakar ya ce, dokar cin zarafin mutane za ta yi daidai da tsarin addinin Islama da zamantakewar al’umma da kuma tsarin shari’a da aiki.

Honarabul Abubakar ya bayyana cewa, a karkashin sabuwar dokar, kwamitocin sun bayar da shawarwari hamsin da bakwai wadanda za su magance matsalolin kowane irin nuna bambanci ko cin zarafin mutane a jihar.

Ya kara da cewa, a karkashin sabuwar dokar, duk wanda aka samu da laifin aikata fyade zai tafi gidan yari ne na rai da rai, kuma wadanda suka taimaka masa wajen aikata laifin su ma za su sami irin wannan hukuncin, Haka zalika, wacce aka yiwa fyaden za a ba ta diyyar da ba ta gaza Naira 500,000 ba.

“Maganar satar mutane hukuncin kisa ne, yayin da batun fyade kuwa shi ne daurin rai da rai, kuma idan wacce aka yiwa fyaden ta kamu da cutar kanjamau, to mai laifin zai sami hukuncin kisa. Duk wanda ya yi yunkurin yin fyade za a hukunta shi a kurkuku na tsawon shekara 14 ba tare da zabin biyan tara ba,” in ji shi.

“Har ila yau, a karkashin dokar, an hana amfani da munanan kalamai da hotunan tsiraici da masu sayar da magungunan gargajiya ke yi, kuma duk wanda aka damke za a hukunta shi,” in ji shi

SendShareTweetShare
Previous Post

Zaman Lafiyar Nijer Shi Ne Na Nijeriya – Buhari

Next Post

Nijeriya Ta Fita Daga Kangin Koma-bayan Tattalin Arziki

RelatedPosts

‘Yan Gudun Hijira Na Fuskantar Matsalar Abinci A Sansanin Jalingo

‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 60, Tare Da Kone Kauye A Zamfara

by Muhammad
1 hour ago
0

Al'ummar garin Ruwan Tofa a karamar hukumar Maru ta jihar...

Rigakafin Korona

Rigakafin Korona: Yau Gwamnoni Za Su Yi Kus-kus

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja   A yau Alhamis, 4...

Borno

Akwai Bukatar Nijeriya Ta Nemo Sojojin Haya Don Yakar ‘Yan Ta’adda – Zulum

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi   An bai wa Gwamnatin...

Next Post
Tattalin arziki

Nijeriya Ta Fita Daga Kangin Koma-bayan Tattalin Arziki

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version