Majalisar Jigawa Ta Amince Da Hukuncin Kisa Ga Masu Fyaden Da Ke Da Kanjamau … Daurin rai-da-rai ga wadanda ba su da cutar

Hukuncin Kisa

Daga Mahdi M. Muhammad,

Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta amince da hukuncin kisa ga masu aikata fyade da ke dauke da cutar kanjamau mai karya garkuwa jiki matukar an gwada wacce suka yi wa fyaden aka ga ta kamu.

Wannan wani bangare ne na kudirin dokar da majalisar ta gabatar don dakile cin zarafin mutane.

Kakakin majalisar, Honarabul Idris Garba Jahun ne ya sanar da wannan a zaman da suka yi a ranar Larabar da ta gabata.

Ya bayyana cewa, zartar da kudirin ya zama doka ya biyo bayan karbar rahoton kwamitin majalisar na harkokin shari’a, karkashin jagorancin dan majalisar da ke wakiltar mazabar Hadejia, Honarabul Abubakar Jallo.

Honarabul Abubakar ya ce, dokar cin zarafin mutane za ta yi daidai da tsarin addinin Islama da zamantakewar al’umma da kuma tsarin shari’a da aiki.

Honarabul Abubakar ya bayyana cewa, a karkashin sabuwar dokar, kwamitocin sun bayar da shawarwari hamsin da bakwai wadanda za su magance matsalolin kowane irin nuna bambanci ko cin zarafin mutane a jihar.

Ya kara da cewa, a karkashin sabuwar dokar, duk wanda aka samu da laifin aikata fyade zai tafi gidan yari ne na rai da rai, kuma wadanda suka taimaka masa wajen aikata laifin su ma za su sami irin wannan hukuncin, Haka zalika, wacce aka yiwa fyaden za a ba ta diyyar da ba ta gaza Naira 500,000 ba.

“Maganar satar mutane hukuncin kisa ne, yayin da batun fyade kuwa shi ne daurin rai da rai, kuma idan wacce aka yiwa fyaden ta kamu da cutar kanjamau, to mai laifin zai sami hukuncin kisa. Duk wanda ya yi yunkurin yin fyade za a hukunta shi a kurkuku na tsawon shekara 14 ba tare da zabin biyan tara ba,” in ji shi.

“Har ila yau, a karkashin dokar, an hana amfani da munanan kalamai da hotunan tsiraici da masu sayar da magungunan gargajiya ke yi, kuma duk wanda aka damke za a hukunta shi,” in ji shi

Exit mobile version