A ranar Laraba ne Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Ibaji, Emmanuel Onuche, bisa zargin aikata ba daidai ba.
Kakakin Majalisar, Aliyu Yusuf, ya sanar da dakatarwar a zaman majalisar na ranar Laraba.
ADVERTISEMENT
- An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano
- Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka
An yi zargin Onuche da aikata wasu ayyuka da ka iya bata sunan gwamnatin jihar kuma an nemi ya sauka daga mukaminsa har sai an gudanar da bincike kan zarge-zargen.
An umarci shugaban karamar hukumar da ya mika harkokin majalisar ga mataimakiyarsa, Mrs Victoria Okolo, har sai an kammala binciken.
Majalisar ta bai wa kwamitin binciken wata daya don kammala aikinsa tare da bayar da rahoto kan matakin da ya dace.














