Majalisar Mahaddata Alkur’ani Ta Yaba Da Shirin Musabakar Mata Da Za A Yi A Sokoto

A kokarin da ta ke na tabbatar da cikakken hadin kan alarammomi a fadin Najeirya, Majalisar Mahaddata alkur’ani ta kasa ta karbi bakuncin guda cikin shuwagabannin Majalisar Mahaddata reshen Jihar Sokoto Alhaji Nasuru Abdullahi Gidadawa wanda ya ziyarci shelkwatar Majalisar Mahaddata alkur’ani ta kasa dake Kano a ranar Lahadin da ta gabata.
Da yake gabatar da jawabin sa a lokacin ganawa da bakon Majalisar reshen Jihar Sokoto, Shugaban Majalisar Mahaddata reshen karamar Hukumar Bichi Gwani Alaramma Abdulmutallib Umar ya bayyana farin cikinsa bisa jaijircewar wannan bawan Allah masoyin alkur’ani da ahlullahi, yace babu shakka majalisar Mahaddata alkur’ani ta kasa zata bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata domin tallafawa harkokin ci gaban karatun alkur’ani.
Da yake gabatar da jawabinsa babban bako kuma jagoran majalisar Mahaddata alkur’ani daga Jihar Sokoto Alhaji Nasuru Abdullahi Gidadawa ya bayyana cewa alarammomi na da muhimmiyar rawar takawa aduk wata harka data shafi alkur’ani, yace yanzu haka batun musabakar alkur’ani ta makarantun sakandiren ‘yan mata wadda Hukumar Rabidatul Islam ke jagoranta, shirye shirye sun kusa kammala wadda mai alfarma sarkin Musulmi Dakta Sa’ad Abubakar III ake sauraro ya sanya rana domin fara wannan kasatacciyar musabaka.
Hakazalika Malam Nasuru Gidadawa ya bukaci Majalisar Mahaddata alkur’ani ta kasa data tabbatar da ganin an bude rassan wannan majalisa a Jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi. A karshe ya tabbatarwa da shugabancin majalisar Mahaddatan samun dukkan hadin kan da ake bukata daga Jihohin da na ambata da farko.
Bayan ganawa da shugabancin Majalisar ne kuma aka jagorancin wakilin Mahaddatan daga Jihar Sokoto zuwa gidan Marigayi Khalifa Isyaka Rabiu domin gabatar da ta’aziyya tare da mika takardar godiya bisa Kyautar alkur’anai da aka rabawa Jihohin kasarnan wadda Sokoto, Zmafara da Kebbi tuni suka yi hafzi da nasu. Gwani Laminu Mahmud Salga sakataren tsare tsare na Majalisar Mahaddata ta kasa ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan Khalifa Isyaka Rabiu a madadin mahaddatan Jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Exit mobile version