Daga Abdullahi Muhammad Sheka
Ranar Juma’ar da ta gabata ne al’ummar Musulmi a fadin duniya suka gudanar da tarukan addu’o’i domin shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1439 bayan Hijira, Shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani na kasa Sheikh Hassan Musa Minna shi ma ya jagoranci gagarumin taron addu’a da kuma saukar Alkur’ani da majalisar ta shirya a fadin kasarnan domin neman Allah Ya kara kawowa Nijeriya zaman lafiya, kwanciyar hankali da yalwar arziki.
Sheikh Hassan Musa Minna ya ce mai alfarma Sarkin Musulmi Dakta Sa’ad Abubakar III ya bayyana ranar Juma’a a matsayin ranar daya ga watan Almuharram, saboda haka Majalisar Mahaddata ta dauki wanann rana ta zama ranar haduwa da ‘yan uwa mahaddata Alkur’ani domin gudanar da addu’o’i tare da jaddada rokon Allah ya karawa shugaban kasa lafiya, haka kuma Majalisar ta hori daukacin Mahaddata Alkur’ani da su shigar da kasa cikin addu’o’i a duk lokutan karatukansu.
Da yake karin haske kan kokarin mai Alfarma Sarkin Musulmi na inganta harkar tsangayu da karatun Alkur’ani, shugaban ya bayyana aniyar alarammomi na ganin sun karbi dukkan wani gyara da kuma shawarwarin da za’a gabatar a lokacin taron da za’a gudanar a Kaduna cikin makon nan, saboda haka Gwani Hassan Musa Minna ya tabbatarwa ‘yan uwa kyakkyawar aniyar shugaban kasa na ciyar da harkar ilimi gaba. shugaban mahaddatan ya bukaci gwamnatoci a matakin kasa da jihohi da su ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki akan harkar tsangayu a duk lokacin da ake shirin kawo wani gyara a harkar tsangayunmu, muna tabbatarwa hukumomin samun hadin kan mu a ko da yaushe” in ji shi.
Shugabann ya yi doguwar nasiha ga jama’a da cewar shigowar sabuwar shekarar Musulunci ba lokaci ne na bushaha ko holewa ba ne, kamata ya yi jama’a su waiwaya baya su ga menene ya faru a shekarar da ta gabata, inda ake bukatar gyara sai a kudiri aniyar gyarawa a cikin wanann sabuwar shekara, kuma dole jama’a su rungumi zaman lafiya da abokan zamansu, domin addinin musulunci ya nuna mana alfanun kyautata zamantakewa. Saboda haka shugaban ya yi addu’ar Allah ya kara mana zaman lafiya a kasarmu baki daya.