Ahmed Muhammed Danasabe" />

Majalisar Malamai A Kogi Ta Raba Zakkar Miliyan N2.5 Ga Mutum 63

Majalisar Malamai

Majalisar Malamai ta Najeriya,reshen jihar Kogi(Council of Ulama) ta rarraba zakkar kudi har naira miliyan biyu da rabi ga mabukata su sittin da uku dake jihar.

Babban sakataren kwamitin kula da rarraba zakka na majalisar, Ustaz Tanko Talle ne ya bayyana hakan a yayin da yake mika kudaden ga mutanen da suka ci gajiyar shirin a ranan Asabar data gabata a garin Lokoja.

Ya bukace su da suyi amfani da kudaden yadda ya kamata inda kuma ya kara da cewa mabukatan da suka ci moriyar shirin rarraba zakkar sun hada da mata talatin da biyu da kuma maza talatin da daya wadanda aka zabo daga kananan hukumomi 21 dake fadin jihar Kogi, inda yace kowanensu ya samu naira 40,000.

Ustaz Tanko Talle ya kuma yi bayanin cewa kwamitin rarraba zakkar ta baiwa mata wadanda suka rasa mazajensu zakkar ganin cewa sun cancanta su ci gajiyar shirin.

Sakataren kazalika yayi bayani cewa wannan shine karon farko da majalisar ta rarraba zakka ga mabukata a jihar.

A lakcar daya gabatar akan muhimmancin bada zakka, mai shari’a Musa Ohu na kotun daukaka kara ta addinin musulunci na jihar Kogi, ya bukaci al’ummar musulmi dasu rika biyan zakka akan lokaci, inda ya jaddada cewa a matsayin shika shikan musulunci na uku, ana bada zakkar ne domin tabbatar da anyi adalci wajen rarraba dukiya a tsakanin al’ummar Musulmi.

Haka shima a nasa jawabin, shugaban bikin kuma tsohon gwamnan farin hula na jihar Kogi, Kyaftin Idris Wada,ya bukaci al’ummar musulmi dasu rungumi akidar bayar wa cikin dukiyarsu kamar yadda Kur’ani mai tsarki ya koyar.

Wada wanda Alhaji Rajab Naibi ya wakilta,yace biya ko bada zakka a matsayin shika shikan musulunci na uku ya zama wajibi ga dukkan al’ummar musulmi ciki har da ma’aikaci mai amsar albashi.

Da ta ke mayar da jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar shirin rarraba zakkar, Uwargida Hajara Yahaya, ta godewa majalisar malaman ta jihar Kogi a bisa kawo musu dauki, tana mai cewa kudaden sun zo akan lokaci, sannan kuma tayi alkawarin cewa da yardan Allah zasu yi amfani da kudaden kamar yadda ya kamata.

 

Exit mobile version