Majalisar Musulmi Ta Koli Ta Nemi A Yi Kidayar Addini

Majalisar Koli ta harkokin Addinin Musulunci ta nemi a yi kidayar adadin mabiya addinai da ke rike da madafun iko da sauran ma’aikatan da ke sassan ma’aikatun gwamnati.

Majalisar ta yi kiran ne a matsayin martani ga kalaman da Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) cewa musulmi sun mamaye galibin abubuwa na kasa.

Sanarwar da mataimakin babban sakataren majalisar, Farfesa Salisu Shehu ya raba wa manema labarai a ranar Larabar da ta gabata, ta ce idan aka yi kidayar za a san su wane ne a kan gaskiya.

“Muna kira ga gwamnatin tarayya ba tare da bata lokaci ba ta fara shirin kidaya na addini ba kawai a bangaren masu mulki ba har da sauran ma’aikatan ma’aikatu domin gano gaskiyar zargin da shugabannin CAN suka yi a lokacin da suka ziyarci shugaban kasa”.

Kungiyar ta kuma nuna mamakinta kan yadda ake muzguna wa Musulmi a yankin kudu alhali kafafen yada labarai sun kame bakinsu sun yi gum, inda ta yi kiran yin adalci a kan komai a kasar nan.

 

Exit mobile version