Majalisar Nasarawa Ta Kafa Kwamitin Binciken Dakatattun Shugaba Da Mataimakin Kananan Hukumomi

A ranar Littinin da ta gabata, majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta kafa kwamitin da zai binciki musabbabin dakatar da Shugaban karamar hukumar Nasarawa da Mataimakin Shugaban karamar hukumar Karu.

Majalisar ta dakatar da wadannan Shugabannin ne a ranar 8/8/2020, bayan sun ziyarci kotun da a ka gabatar da shari’a tsakanin tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar da ‘yan majalisan.

Majalisar ta zarge su da nuna goyon baya ga nasarar da tsohon Sakataren Gwamnatin, Alhaji Ahmad Tijjani Aliyu ya samu.

Majalisar ta nada mutum bakwai karkashin jagorancin Dakta Ibrahim Peter Akwe, a matsayin wanda zai jagoranci binciken na tsawon wata uku.

Wadanda kwamitin zai yi aiki a kansu sun hada da dakataccen Shugaban karamar hukumar Nasarawa, Alhaji Muhammad Sani Ottos, da mataimakin Shugaban karamar hukumar Karu, Lawal Yakubu Karshi.

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Honorabul Balarabe Abdullah, ya bukaci kwamitin da ya yi aikin da a ka sanya shi cikin tsari da gaskiya. Ya tabbatar ya yi bincike ta yadda kowa zai tabbatar da an yi adalci cikin lamarin.

Duk da cewa an dakatar da Shugabannin ne ba tare da yin bincike a kan laifin su ba tun da farko. Kuma har ya zuwa yanzu ba a ba su damar komawa aikin su ba, kuma ba a bayyana iya adadin lokacin da za su yi a dakace kafin komawa bakin aiki ba, sannan ba kuma korar su a ka yi ba.

Exit mobile version