Daga Muhammad Awwal Umar,
Majalisar dokokin Neja ta bayyana kudurinta na samar da dokar da ta shafi garkuwa da jama’a na hukunta mutanen da ke tsegunta wa ‘yan bindiga bayanan jama’a a jihar.
Shugaban majalisar dokokin, Rt. Hon. Abdullahi Bawa Wuse ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci majalisar fadar gwamnatin jihar dan jajantawa gwamna kan harin daliban makaranta tare fasijojin NSTA da ake garkuwa da su a halin yanzu.
“Mun tsayar da wannan satin, za mu gyara akan dokar da ta shafi garkuwa da jama’a da mu sanya masu baiwa ‘tan bindiga bayanai dan hukunta su.”
Majalisar ta shawarci gwamnatin da ta shirya taruka da sarakuna kuma ta ba su damar sanya ido akan kula da shigar baki a yankunan su, shugaban majalisar yace majalisar dokokin jihar a shirye ta ke dan taimakawa da duk hanyar da ta dace wajen kawo karshen rashin tsaro a jihar.
Shugaban majalisar ya yi tir da wannan nummunar barnar da ya faru a Kagara da kuma wasu kauyukan, ya kara da cewar akwai bukatar kowa ga Allah dan sanun nafita.
A bayaninsa, gwamna Abubakar Sani Bello ya yabawa majalisar akan irin nuna goyon bayanta ga jihar kuma yayi na’am da waiwayo dokar da ta shafi garkuwa da jama’a dan hukunta masu tseguntawa ‘yan bindiga bayanan jama’a.
Ya nuna damuwarsa akan hare-haren da ‘yan bindigar ke kaiwa wasu sassan jihar nan, kuma ya bada tabbacin zai dauki matakan da suka dace dan dawo da dalibai da fasinjojin da ake garkuwa da su ga iyalansu.
” Muna cigaba da daukar matakan sanya ido dan sanin asalin inda aka samo tushen matsalolin rashin tsaron da muke fuskanta, da irin matakan da ya dace mu dauka”.
Gwamna ya bayyana cewar akwai taruka da dama da muka yi da sarakuna, wanda muna ba su damar bin matakan da suka dace wajen sanya ido akan yadda ake gudanar harkokin yau da kullun a yankunan su kuma su rika sanar da hukumomin da suka dace, kuma za mu cigaba da shirya tarukan da su.