Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Bude Makarantu

kasafin

Kwamitin majalisar wakilai kan harkar ilimi ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da batun sake bude makarantu a gobe Litinin 18 ga watan Junairu. Bude makarantu a halin yanzu zai kawo babban nakasu ga yaki da cutar Korona, a cewar kwamitin.

Shugaban kwamitin, Julius Ihonvbere, ya ce gwamnati bata tuntubi majalisar ba kafin sanar da ranar bude makarantu, don haka ta bukaci Gwamnatin ta dakatar da batun komawar daliban Makarantu har zuwa nan da watanni uku masu zuwa.

Exit mobile version