Majalisar Wakilai, ta kafa wani kwamitin na musamman da zai duba yadda ake amfani da kuɗaɗen Kirifto da kuma POS, waɗanda ke shafar tattalin arziƙi, tsaro, da harkokin kuɗi a Nijeriya.
Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen, ya ce an kafa kwamitin ne saboda yawaitar damfara, laifuka a yanar gizo, da amfani da kuɗin Intanet wajen aikata miyagun ayyuka.
- Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026
- Minista Nnaji Ya Yi Ƙarar Jami’ar UNN Kan Rikicin Takardun Kammala Makaranta
Ya bayyana cewa, duk da cewa kuɗin Kirifto na iya taimakawa wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa, yana kuma da barazana ta fuskar safarar kuɗaɗen haram, ta’addanci, da rashin tsari na doka.
Saboda haka, kwamitin zai tsara dokoki da za su daidaita harkar da kuma kare masu amfani da kuɗin.
Shugaban kwamitin, Olufemi Bamisile, ya ce za su yi aiki tare da hukumomin gwamnati kamar Babban Bankin Nijeriya (CBN), Hukumar Tsaro ta Kuɗi (SEC), EFCC, da ƴansanda domin tabbatar da cewa ci gaban fasahar kuɗi bai zama barazana ga tsaron ƙasa ba.
Ya ƙara da cewa kwamitin zai gudanar da zaman jin ra’ayoyi daga masana da sauran masu ruwa da tsaki kafin ya kammala rahotonsa.