Majalisar Zartarwa Ta Amince Da Dawo Da Tsarin Musayar Fili Na Abuja  

Sanatoci

Daga Abubakar Abba

A jiya Laraba ne, Majalisar Zartarwa ta Gwamnatin Tarayya ta amince wa mahukunta Babban Birinin Tarayyar Abuja, da ya dawo da tsarin musayar fili.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci zaman Majalisar da aka gudanar a fadar Shugaban kasa da ke Abuja,

Ministan babban birinin tarayyar Abuja Mohammed Bello ne ya bayyana hakan a yayin da yake tattaunawa da manema Labarai a fadar Shugaban kasa jim kadan bayan  kammala zaman da majalisar ta yi.

Tsarin wanda ya kai na kimanin Naira tiriliyan daya a karkashin gwamnatin tarayya da ta gaba, an tsara shi ne don a rage karancin gine -ginen gwamnatin ta hanyar yin musayar fili da masu zuba jari masu zaman kansu, wadanda daga baya,  za su samar da gine-ginen.

A cewarsa, an amnince ne bayan da aka gabatar wa da majalisar da takardar kan maganar a lokacin zamanta.

Ministan ya bayyana cewa,  an kuma yi canje-canje kan ainahin takardar a tsakanin ko wanne bangare daya.

Exit mobile version