Khalid Idris Doya" />

Majalisar Zartarwa Ta Amince Da Kudirin Kudi Na 2020

Sanatoci

A zaman Majalisar Zartaswar Nijeriya (FEC), wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a jiya Laraba, majalisar ta amince da kudurin kudi na 2020 domin tallafa wa kasafin 2021 tare da neman rage wa kamfanoni nauyin biyan haraji.

Ministan kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed, ita ce ta shaida hakan bayan kammala ganawar FEC din na jiya ga ‘yan jarida, ta shaida cewar kudurin an tsara ne domin kawo sauye-sauye ga dokokin haraji na kasa.
Ministar wacce take zantawa da ‘yan jaridan tare da abokan aikinta, ta ce da zarar kudurin ya zama doka ba zai kai ga karin kudin haraji a fadin kasar nan ba sam sam, illa dai za a samu sauye-sauyen da zai kai ga inganta sashin kudin harajin.
Da take karin haske kan ababen da wannan kudirin ya kunsa, Ministar ta ce daga cikin manufar samar da kudirin har da neman a saukaka ma wasu kamfanoni nauyin haraji, musamman ma kanana da matsakaitan kamfanoni.
Tana mai cewa tunin ma an riga an rage wasu harajin, “A kudurin kudi na 2019, mun rage haraji kashi 30 zuwa 20 ma kamfanoni.”
Zainab ta sake bada tabbacin cewar sam wannan matakin ba zai kai ga kara kudin haraji ba a fadin kasar nan, “Wannan ba lokaci ne na kara kudin haraji ba.”
Kudurin wanda kwanan nan za a mika shi ga majalisar kasa domin neman sahalewa da amincewa domin ya zama doka.

Exit mobile version