Connect with us

LABARAI

Majalisar Zartaswa Ta Aminta Da Kashe Wa Ofishin EFCC Naira Miliyan 500

Published

on

A jiya Laraba ne majalisar zartaswa FEC ta amince da bukatar da hukumar EFCC ta neman na kashe Naira Miliyan 500 don gyare gyare a sabon ofishisu da a aka kaddamar kwanakin baya.

Kwanana n ne Hukumar EFCC ta tare a sabon hedikwatar hkumar mai hawa 10 da aka gina a babban birnin kasar nan Abuja.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin jami’in watsa labarai na Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu,  atattaynawasa da ‘yan jarida bayan kammala taron majalisar zaetasawar wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya jagoranta, ya ce, hukumar EFCC ta samu amince da sayan kwamputa 700 da Laptos 100 da kuma Laser printers 25 a kan kuxi Naira Miliyan 459.

Mista Shehu ya kuma kara da cewa, an kuma amince da bukatar EFCC na sayan motoci 15.

“Suna faxaxa aikinsu ne a saboda haka suna bukktar motoci don gudanar da ayyukansu, dukkan motocin daga cikin gida aka saye su,” inji shi.

Mista Shehu ya kuma ce, majalisar ta kuma amince da sayen jigin ruwa na sintiri guda 5 don amfanin hukumar ‘Nigerian Ports Authority’ dake Marina, ta jihar Legas.

“wannan don samar da tsaro ne a gabar ruwar kasar nan,” inji shi.

Daya ke karin bayani, Ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu, ya ce majalisar ta kuma amince kuxaxen gyaran Dam na Cham mai  faxin heka 100 din akin noman rani a karamar huykumar Balanga ta jihar Gombe.

“Wannan yana cikin shirinmu na kammmala dukkan ayyukan da muka gada daga gwamnatoticin baya, an fara aikin ne a shekarar 2011 amma rasgin kuxaxe ya kawo wa aikin cikas,” inji shi.

Ministan y ace, an dakatar da aiki ne a lokacin ana kusan kasha 65 da kamalawa, amma yanzu an sake tataunawa a kan farashin aikin gaba xaya tar da xan kwangilar.”

Ya ce ya kawo karin naira Miliyan 612 don kammala aikin gaba xaya, ya kuma kara da cewa Hkumar ‘Upper Benue Riber Basin Debelopment Authority’ ke lura da gudanar da ayyukan.

“da farko an gida dam xin ne a shekarar 1982, daga baya aka kuma sake ginawa, kuxin farko da aka shirya gina dam xin ya kai naira Miliyan 832, a shekarar 2011 a ka sake bayar da kwangilar  gina dam xin.”

Mista Suleiman ya kuma yi karin bayani a kan kikddigar barnar da ambaliya ta yi afaxin kasar nan, ya ce, a halin yanzu an fita duk wata baraza daga ambaliya a faxin kasar nan a halin yanzu, sai dai in wani abu da bamu sani bay a faru, inji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: