Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Shugabannin (Kakaki) Majalisun Dokokin Jihohin Kasar nan sun kare taron su na tuntubar juna a garin Bauchi, inda suka kafa kwamiti da za duba yiwuwar wanzar da canje-canje a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan domin yin kwaskwarima ga wasu batutuwan da suke ganin kasar za ta ci gaba idan aka waiwayesu.
Taron na Kakakin Majalisun Dokoki na jihohi 36 na kasar nan ya bayyana cewar, an baiwa kwamitin hurumin yin nazari kan bukatun canje-canje na majalisun, da kuma gabatar da tsarin nasu majalisun ga kwaryar sake duba tsarin mulki kasa dake gudana a halin yanzu.
Shugaban Zaure Majalisun Dokokin Jihohin wanda kuma shi ne Kakakin Majalisar Jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Yakubu Sulaiman shine ya bayyana kudirorin taron wanda ya duba lamura masu yawa da suka jibanci kasar nan.
Gaba-gaba cikin lamuran shine na matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar nan, a inda taron ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta mayar da hankali kan wannan lamari domin ya tafi bai daya da taswirar tsirurukan kasar nan
Rt. Hon. Abubakar Suleiman ya bayyana cewar, taron wanda aka gudanar a Otal da Makwatan Hazibal dake cikin garin Bauchi ya karkata bakin sa ne wajen baiwa kasar nan tsaro ta hanyar hadin kai wanda ya kunshi hukumomin tsaro da al’ummomin kasa doin shawo kan lamarin.
Jawabin bayan taro taron ya kuma bukaci daukacin Majalisun Dokoki na jihohin kasar nan da su amince da dokar kasafta kudaden rabo na kasar nan yadda zai wanzar wa majalisun dokoki da fannonin shari’a cin gashin kansu.
Taron, wanda Kakaki na Majalisun Dokokin jihohi 36 da mataimakan su daga wasu jihohi suka halarta ya kuma nemi kungiyar ma’aikatan majalisun dokoki na jihohin kasar nan (PASAN) da su mayar da wukaken su zuwa kube dangane da koke-koken, ko bukace-bukacen da suke da su.
Kamar yadda jawabin bayan taron ya bayyana, tuni zauren Kakakin Majalisun Dokokin na jihohi ya kafa wani ingataccen kwamiti domin zama da kungiyar ma’aikatun majalisun da zummar shawo kan matsalolin nasu.
Taron na Bauchi ya kuma jinjina wa Gwamnan Jihar, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad bisa yadda gwamnatin sa ta karbi bakwancin shugabannin majalisun dokokin na jihohin tarayyar Nijeriya, iya tsawon badoncin su a garin Bauchi.
Daga nan, sun nuna damuwarsu matuka kan matsalolin tsaro da suke addabar kasar nan, inda suka yi kira da a dauki matakan da suka dace wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummomin kasar nan.