Ibrahim Muhammad" />

Makanikan Kungiyar NATA Masu Gaskiya Da Rikon Amana Ne

Kungiyar masu fasahar gyaran motoci ta kasa reshen Sharada ta yi bikin cikarta shekara daya tare da karrama wasu fitattun mutane da suke bada gudummuwa ga cigabanta.
Da yake zantawa da manema labarai a yayin taron Shugaban kungiyar NATA na kasa Injiniya Magaji Muhammad Sani ya ce, makanikan kungiyar NATA masu gaskiya ne da amana koda yaushe a matsayinsu na shugabanni suna horonsu da riko da gaskiya da amana.
Ya yi nuni da cewa a baya idan harka ta hadaka da makanikai sai a roka kokwanton gaskiyarsu amma yanzu wannan ya kau a kungiyar NATA mambobinsu masu gaskiya ne da rikon amana takai ma ana shedarsu da mayar da kudade da aka manta a mota.
Injiniya Magaji Muhammad ya nuna godiyarsa ga Allah bisa cigaba da hadin-kai da zaman lafiya da NATA take dashi sannan ya yaba wa reshen kungiyar na sharada bisa wannan taro data shirya na cikarta shekara daya da kuma karramawa da ta yi musu hakan wani abune na tarihi.
Ya ce, NATA kungiya ce dake tafiya da sauyin zamani da yake ana yawan samun sauyi a harkar motoci shi yasa suke tura yan kungiyar samun horo kala-kala da hadin gwiwar Gwamnatin tarayya ta karkashin ma’akatar ciniki da kuma kamfanin Ammasco.
Ya ce, a nan Gwamnatin Kano ta dauki nauyin makanikai an horas da su kan gyaran motoci har da wadanda aka tura koyon gyaran manyan motoci aka basu tallafi na kudi da kayan aiki bayan garejin zamani da aka gina a sassan Kano.
Injiniya Magaji Muhammad Sani ya yi kira ga yan NATA da sauran masu fasahar gyaran ababen hawa su tsaya a kan gaskiya da rikon amana hakan zai kaisu ga nasara a kowane mataki.
Shima a nasa bangaren shugaban NATA reshen Sharada ya bayyana cewa sun shirya taron ne domin karrama wasu muhimman mutane da kuma bayyana nasarori da suka samu tun bayan zabarsu a shugabancin kugiyar a shekara daya.
Ya ce, cikin nasara da sukk samu sun horar da yara fa suka kai 60 a wannan yanki na sharada tareda kai dauki ga wasu yan kungiyar da suka fada wata matsala
Injiniya Mustapha ya yi kira ga Gwamnati ta basu hadin kai domin suna da niyya ta koyawa dinbin matasa wannan sana’a ta gyaran motoci dan rage masu zaman kawai.
Injiniya Mustapha ya ce, suna kokarin hada kai da jami’an tsaro dan kyautata cigaban sana’arsu.

Exit mobile version