Muhammad Awwal Umar" />

Makantata Ba Ta Hana Ni Sauke Kur’ani Ba – Hafsat

HAFSAT SULAIMAN mai lalurar makanta ce, wacce ta ce duk da wannan lalurar a ka haife ta, amma hakan bai hana ta ikon sauke karatun Alkur’ani ba. A zantawarta da wakilin LEADERSHIP A YAU, MUHAMMAD AWWAL UMAR, a Kontagora ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta a rayuwarta da ma yadda ta faro karatun addini. Ga hirar kamar haka:

 

Ya ya rayuwarki ta fara?

An haife ni nan garin Kontagora, kuma cikin hukuncin ubangiji da wannan lalurar makantar a ka haife ni.

 

Ganin sau tari idan an haife yaro da irin wannan lalurar ba a ciki mai da hankali wajen ba shi ilimi ba, shin ke ya abin ya ke a wajen ki?

Da farko bayan na taso mahaifina ya sanya ni makarantar allo, duk da cewar mahaifina bai samu zarafin sa ni makarantar boko ba, bai sa na yi sanyin guiwa ba, ina makarantar allo na dan wani lokaci sai na bari na dawo nan inda ni ke a yanzu da har Allah Ya kai ni a wannan matakin da ni ke a yanzu.

 

Shin ita wannan Islamiyyar ta masu lalurar makanta ce?

Islamiyya ce ta masu gani, kusan dukkanin daliban ba mai wani nakasa a zahiri.

 

Ganin a kowani lokaci tsarin Islamiyya, tsari ne wanda ake rubutawa a allo, shin ke ya ki ke fahimtar karatun?

Ai bayan an rubuta, sai a karanta min in haddace.

 

Zan so ki min karin bayanin yadda ki ka faro karatun zuwa yanzu.

Lokacin da na ke makarantar allo, akan rubuta min ne a karamin allo a ba ni, sai a karanta min. Abinda aka rubuta din nan shi za a karanta min ina haddacewa, bayan na dawo nan Islamiyyar kuma su abokan karatuna idan sun bude Al-kur’ani ko wani littafi na addini da za a karantar da mu to ni daman yana cikin kwakwalwata tunda ni hadda ni ke yi, domin indai za a karanta koda sau daya ne to zan hadda ce shi.

 

Bayan Al-kur’ani akwai wasu littafai da ki ka karanta?

Sosai kuwa, domin na karanta Fikihu kuma na karanta Tauhidi, na karanta Sirrah da Nahawu.

 

A lokacin karatun naki wadanne irin kalubale ki ka samu ganin ki na karatu tare da masu idanu?

Ban fuskanci wani kalubale ba gaskiya, an bani kulawa sosai wajen karatuna ma. Malamai na da Iyaye na sun kula ni sosai, koda ni ke karatu ba wani matsala sai dai in an yi laifi a aji a dan yi bulala haka, ka ga ai wannan tarbiya ce ta kwarai domin a nuna maka kuskuren ka gyara dan gobe, amma maganar kalubale kam babu shi.

 

Ta ya ki ke zuwa makarantar, ki na kani ko wata kawa da ke maki jagora ne zuwa makarantar?

Babu, ni kadai ke kai kaina makaranta.

 

Da ma kin san hanyar makarantar ne?

Sosai kuwa, duk indai wani kware da kwazazzabo yake ko yashi indai na bi sau guda zai kiyaye.

 

Mai karatu zai so sanin ko ki na amfani da zuciyarki ne, ki ke fahimtar yadda hanya ta ke idan ki na tafiya.

Idan ina gani da zuciya ko ban gani da zuciya ban sani ba, indai na tashi zuwa wuri kama hanya kawai na ke yi sannu a hankali har in isa inda na ke son zuwa.

 

Wane irin kwarin gwiwa ki ka samu a wajen mahaifanki har ki ka kai wannan matsayin na sauke Alkur’ani a yau?

Wallahi gaskiya, Alhamdulillah. Domin idan lokacin zuwa makaranta ya yi ban tafi ba, za ka ga an nuna min damuwar hakan. Idan ma mahaifana ba sa gida suka dawo suka tarar da ni a gida ban tafi makaranta ba, sai sun tambaye ni dalilin rashin zuwa ta makaranta, wanda wannan kulawar ita ce ta kai ni ga wannan nasarar ta yau da na samu a rayuwa ta. Na samu tallafi domin an kula da neman ilimina yadda ya kamata.

 

Ganin wannan lalurar ta makanta babba ce, domin da ita a ka haife ki, shin kin taba jin akwai lokacin da za ta hana ki neman ilimi a rayuwarki?

Ni ban taba samu damuwa ba, domin ba ta hana ni neman ilimi ba domin ba a kwance na ke ba, ina iya zuwa ko ina da kafa ta, ka ga ke nan ba za ta hana ni neman ilimin da na sanya a gaba ba ko kadan, bai ba ma zai faru ba, domin shi mahalicci ai yasan da ni kuma haka yake bukata ta, dan haka ina godiya sosai ga Allah da Ya halicce hakan kuma ya ba ni mahaifa da suka rungume ni hannu biyu.

 

Sau tari yara kan tsangwami wani mai nakkasa idan ya taso a cikinsu. Shin ke kin taba samun tsangwama a tsakani abokan karatunki?

Gaskiya ban taba samu ba, domin suna taimaka min kuma muna da kyakkyawar fahimta a tsakanin mu.

 

Wani kira ki ke da shi ga ‘yan uwanki musamman yaran da a ka haife su da wata nakasa a jikinsu dan gane da neman ilimi?

Kirana a nan musamman ga Iyaye ma, su sani haihuwar yaro da nakasa ba gazawa ba ce, domin in an kula da shi zai iya zama jigo ko wani abin alfahari  a rayuwa kamar kowani dan da aka haifa. Musamman su daure su kula da bashi kulawa da tarbiya domin ribar biyu ce akwai ta duniya kuma akwai lahira wanda wannan kuma sai mai rabo da ya yi Imanin da cewar Allah Ya ba shi wannan arzikin ne domin ya jaraba Imanin sa, dan haka ina kira ga Iyaye ba wai sai nakasasshe ba har lafiyayyen idan an kula da shi an bashi tarbiya an kuma ilmantar da shi zai anfani al’umma gaba daya.

 

Ganin yanzu kusan mahaifanki ne ke kula da ke. Wane kira ki ke da shi ga gwamnati da masu hannu da shuni wajen kulawa da yara masu nakasa?

Lallai da gwamnati da masu hannu da shuni zasu taimaka wajen kulawa da yara masu nakasa ta hanyar neman ilimin su da sana’a, da an shawo kan matsalar barace-barace a cikin al’umma. Misali ni ka ga mahaifina ya taimaka min sosai don ko a dakin mu wajen mahaifiyarmu mu goma ne amma hakan bai hana ba ni kulawa ta musamman ba, idan mahaifina yana da halin hakan ba kowani uba ne ke da irin wannan halin ba, idan gwamnati za ta shigo masu hannu da shuni zasu shigo a samar da makarantu dan nakasassu a koyar da su karatu kuma a koya masu sana’a ina da tabbacin kowa zai iya tsayawa da kafarsa ai.

 

Yanzu Malama Hafsat, me ye burinki a rayuwa nan gaba?

Burina in cigaba da karatu, domin ilimi ai baya kadan. Domin shi ilimi ai ba iya kai karshen sa, karatu dai musamman na addini yanzu ma aka fara shi da yardar Allah.

 

Malama Hafsat, me ye fatanki ga ‘yan uwanki matasa masu nakasa da ma lafiyayyun?

Fatana, Allah Ya kara mana kwarin guiwar cigaba da neman ilimi domin shi ne gishirin rayuwa. Domin idan kana da ilimi ba za ka walakanta ba a rayuwar duniya da lahira, ina rokon Allah yadda Iyayena su ka jajirce a kaina su ma sauran Iyaye su jajirce a kan ‘ya’yansu wajen kulawa da tarbiya da kula da ilimin ‘yayansu.

 

Exit mobile version